Kwamishina ya yanke jiki ya fadi ya mutu yayin gabatar da kasafin kudi a Enugu

Kwamishina ya yanke jiki ya fadi ya mutu yayin gabatar da kasafin kudi a Enugu

- Kwamishinan sufuri na jihar Enugu, Matthias Ekweremadu ya mutu

- Ekweremadu ya yanke jiki ya fadi ne yayin gabatar da kasafin kudin ma'aikatarsa

- An garzaya da shi asibiti nan take inda daga bisani likitoci suka tabbatar da ya mutu

Mista Matthias Ekweremadu, kwamishinan sufuri na jihar Enugu ya riga mu gidan gaskiya.

Ekweremadu ya rasu ne a ranar Alhamis bayan ya yanke jiki ya fadi yayin gabatar da kasafin kudin ma'aikatarsa a gaban kwamitin sufuri ta majalisar dokokin jihar Enugu, The Cable ta ruwaito.

Kwamishina ya yanke jiki ya fadi ya mutu yayin gabatar da kasafin kudi a Enugu
Kwamishina ya yanke jiki ya fadi ya mutu yayin gabatar da kasafin kudi a Enugu. Hoto: @thecableng
Source: Twitter

An garzaya da shi asibitin Niger Foundation cikin gaggawa inda daga bisani aka sanar da cewa ya rasu.

DUBA WANNAN: 'Mu ma abin ya ishe mu', 'Yan Bayelsa sun nemi a fattaki makiyaya daga jiharsu

Ogbuagu Anike, kwamishinan labarai da ya sauka daga mulki a Enugu, ya tabbatar wa majiyar Legit.ng rasuwar kwamishinan.

Marigayin dan uwa ne ga tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Eke Ekweremadu.

Marigayi Ekweremadu ya yi aiki a matsayin shugaban karamar hukumar Aniri kafin a zabe shi dan majalisar dokokin jihar Enugu a shekarar 2015.

KU KARANTA: Jaruman mutanen gari sun fattaki 'yan bindiga a rugar makiyaya a Kaduna

Ya zama bulaliyar majalisa bayan haka Ifeanyi Ugwuanyi gwamnan Enugu ya nada shi a matsayin kwamishinan sufuri a 2019.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel