Ba makiyaya bane suka bankawa makarantar sakandare wuta, Gwamnatin Kogi

Ba makiyaya bane suka bankawa makarantar sakandare wuta, Gwamnatin Kogi

- Gwamnatin jihar Kogi ta karyata jita-jitar da ake yadawa na cewa makiyaya ne suka kona makarantar sakandare ta Iluke Bunu

- Sanarwar da kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya fitar ta ce binciken da aka fara ya nuna kona daji ne ya yi sanadin gobarar

- Fanwo ya ce hukumomin tsaro na cigaba da zurfafa bincike don haka ya yi gargadi kan yadda jita jitar da ka iya tada zaune tsaye a jihar

Gwamnatin jihar Kogi ta karyata rahotannin da ke cewa makiyaya Fulani ne suka kona makarantar sakandare ta Illuke Bunu inda ta ce kona daji ba bisa ka'ida bane ya janyo gobarar, Vanguard ta ruwaito.

Hakan ne kunshe ne cikin sanarwar da kwamishinan watsa labarai na jihar, Mista Kingsley Fanwo ya fitar mai taken, 'Rahoton farko game da kona makarantar sakandare ta Iluke Bunu.'

Ba makiyaya bane suka bankawa makarantar sakandare wuta, Gwamnatin Kogi
Ba makiyaya bane suka bankawa makarantar sakandare wuta, Gwamnatin Kogi. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Sanarwar ta kuma ce gwamnatin za ta cigaba da zurfafa bincike yayin da ta yi tir da wadanda ke gaggawar alakanta lamarin da wani sashi na al'umma.

DUBA WANNAN: Kwamishina ya yanke jiki ya fadi ya mutu yayin gabatar da kasafin kudi a Enugu

"Konewar makarantar sakandare ta Iluke Bunu abu ne da gwamnati ta damu da shi.

"Gwamnatin jihar tana tir da gaggawan da wasu suka yi na cewa makiyaya Fulani ne suka kona wani sashi na makarantar. Irin wannan rahoton mara tabbas na iya tada tarzoma a jihar.

"Binciken da muka fara gudanarwa ya nuna cewa kona daji ba bisa ka'ida ba da wasu mutane biyu da ba a gano su ba suke yi ne ya janyo gobarar.

"A yayin da muke cigaba da bincike kan sababin gobarar, muna gargadi game da yin kalaman da za su iya kawo cikas ga zaman lafiyar da ake yi tsakanin kabiloli a jihar Kogi.

"Al'ummar Kogi suna zaman lafiya da Fulani, Bassa, Nupawa da sauran mutane da ke zaune ko yin kasuwanci a jihar," a cewar wani sashi na sanarwar.

KU KARANTA: Alkali ya yanke wa matashi hukuncin daurin rai-da-rai saboda haike wa wata a Jigawa

Ma'aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha da Shugaban karamar hukumar Kabba/Bunu da mai bada shawarar kan tsaro na jihar sun bukaci hukumomin tsaro su binciko wadanda suka aikata abin don fuskantar sharia.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel