Nan da 2025, kashi 30 na motocin Najeriya da lantarki zasu rika amfani, Jelani Aliyu
- An hada mota maras amfani da man fetur ta farko a Najeriya
- Hukumar cigaban motoci a Najeriya ta bayyana motar kirar Hyundai Kona ranar Juma'a
- A cewar shugaban hukumar, nan ba da dadewa ba Najeriya za ta koma hawa motacin lantarki
Gwamnatin tarayyar Najeriya na harin tabbatar da cewa nan da shekaru hudu masu zuwa, kashi 30 na motocin da za'a rika amfani da su a Najeriya su kasance masu amfani da wutan lantarki.
A jawabin da yayi kaddamar da motar lantarki ta farko da aka hada a Najeriya, shugaban hukumar zane da cigaba motoci a Najeriya, Jelani Aliyu, ya bayyana cewa lokacin amfani da mota mai lantarki a Najeriya yayi.
Aliyu ya ce ba za'a bar Najeriya a baya ba yayinda duniya ke cigaba wajen daina amfani da motoci masu amfani da man fetur, Daily Trust ta ruwaito.
Kawo 2019, Aliyu ya ce gwamnatin tarayya ta zuba kudi $1 billion a masana'antar motoci.
Shugaban hukumar ta ce kamfanin Stallion wacce ke kan gaba wajen samar da irin wadannan motoci ta zuba hannun jarin $300 million a Najeriya.
Hakazalika, ministan masana'antu, kasuwanci da hannun jari, Otunba Adeniyi Adebayo, ya ce motoci masu amfani da lantarki zasu taimakawa wajen rage amfani da man fetur da kuma lalacewar yanayi
Ya ce motar Hyundai Kona da lantarki take amfani dari bisa dari, babu bukatar fetur ko kadan.
KU KARANTA: Buhari zai kaddamar da ginin layin dogon Kano-Maradi, Kano-Dutse
DUBA NAN: Tsagerun yan bindiga sun fi sauraron Sheik Ahmad Gumi fiye da gwamnati, Lai Mohammed
Mun kawo muku rahoton cewa shugaban hukumar zanen motoci a Najeriya (NADDC), Jelani Aliyu, ya bayyana kerarriyar mota mai amfani da lantarki ta farko Najeriya.
Bikin bayyana motar kirar 'Hyundai Kano' ya auku ne ranar Juma'a a Abuja kamar da yadda hukumar ta sanar a shafinta na Tuwita.
A cewar sanarwa, za'a yi bikin baja kolin motar na tsawon kwanaki uku daga ranar 5 ga Febrairu zuwa 7 ga Febrairu a wurare daban-daban.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng