Buhari zai kaddamar da ginin layin dogon Kano-Maradi, Kano-Dutse
- Bayan kammala Lagos-Ibadan, za'a fara ginin layin dogo daga Kano zuwa Maradi
- Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan yarjejeniyar ginin layin dogon tsakanin Najeriya da Nija
- Wannan shine na biyu da za'ayi a yankin Arewacin Najeriya
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da ranar kaddamar da ginin layin dogo daga jihar Kano zuwa Maradi a jamhurriyar Nijar, da kuma Kano zuwa Dutse a jihar Jigawa.
A cewar Ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, Buhari da kansa zai kaddamar da fara ginin ranar Talata 9 ga watan Febrairu, 2021.
Amaechi ya sanar da haka a shafinsa na Tuwita.
"Muna farin ciki sanar da kaddamar da ginin layin dogon Kano-Maradi, Kano-Dutse ranar Talata," yace.
"Shugaban kasanmu, Muhammadu Buhari zai kaddamar. An fara aiki."
KU DUBA: Gwamnatin Kano ta kai Sheikh AbdulJabbar Kotu, ta samu izinin kulle Masallacinsa da hanashi wa'azi
A bangare guda, gwamnatin tarayyar Nigeria, FG, ta sanar da fara tattaunawa da wakilar kungiyoyin kwadago a kan yadda za a kara kudin dakon man fetur daga N7.51 zuwa N9.11 duk lita.
Wannan tsarin na nufin karin kashi 21.30 cikin dari a kudin dakon man fetur din.
An bada wannan sanarwar ne bayan taron kungiyar masu motocin haya na kasa da ake yi a Zuma Rock Resort, a babban titin Abuja zuwa Kaduna, The Punch ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng