Cikin hotuna: An hada mota mai amfani da lantarki ta farko a Najeriya
Shugaban hukumar zanen motoci a Najeriya (NADDC), Jelani Aliyu, ya bayyana kerarriyar mota mai amfani da lantarki ta farko Najeriya.
Bikin bayyana motar kirar 'Hyundai Kano' ya auku ne ranar Juma'a a Abuja kamar da yadda hukumar ta sanar a shafinta na Tuwita.
A cewar sanarwa, za'a yi bikin baja kolin motar na tsawon kwanaki uku daga ranar 5 ga Febrairu zuwa 7 ga Febrairu a wurare daban-daban.
Jawabin yace: "Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola; Dirakta Janar na NITDA, Kashifu Inuwa da sauran manyan baki a bikin bayyana motar Hyundai Kona mai amfani da lantarki da aka hada a Najeriya."
"Za'a iya bibiyan motocin a wurare irinsu Silverbird Entertainment Center, Banex Plaza, AYA junction Asokoro, Transcorp Junction, Majalisar dokokin tarayyada Federal Secretariat.”
Kalli hotunan:
Asali: Legit.ng