Tsagerun yan bindiga sun fi sauraron Sheik Ahmad Gumi fiye da gwamnati, Lai Mohammed
- Gwamnatin tarayya ta nuna amincewarta da jihadin da Sheikh Ahmad Gumi yake yi
- Sheikh kuma ya fara shiga dazuka domin tattaunawa da yan bindigan da suka addabi mutane
- Ziyarar karshe da Gumi ya kai itace zuwa karamar hukumar Shinkafi a Zamfara
Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, a ranar Juma'a, ya ce ba matsala bane shahrarren malamin addini, Sheikh Dr Ahmad Gumi, ya shiga tsakanin yan bindiga da gwamnati a jihar Zamfara.
Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a shirin 'This Morning' na tashar TVC.
Ya ce gwamnati na amfani da wasu sabbin hanyoyin magance matsalar tsaron Najeriya, kuma da yiwuwan tsagerun yan bindigan zasu fi sauraron Malamin addini fiye da gwamnati.
A ranar Talata, hotunan Sheikh Ahmad Gumi sun bayyana inda ya shiga karamar hukumar Shinkafi da Gummi domin zama da yan bindiga.
Legit Hausa ta ruwaito muku cewa Sheikh Ahmad Gumi ya shiga dazuka a jihar Kaduna da jihar Zamfara domin yiwa yan bindiga wa'azi su ajiye makamansu.
KU KARANTA: Gwamnatin Kano ta kai Sheikh AbdulJabbar Kotu, ta samu izinin kulle Masallacinsa da hanashi wa'azi
Mun kawo muku labarin cewa Sheikh Dr. Ahmed Mahmoud Gumi ya bada labarin tafiyar da ya yi zuwa sansanin wasu ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
Ganin yadda ake fama da matsalar rashin tsaro a Arewa maso yammacin Najeriya, babban malamin ya shiga inda ‘yan bindiga su ke, ya na lallabarsu.
Da yake yi wa gwamnan Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, bayanin abin da ya gani, Malamin ya bayyana cewa tsagerun ‘yan bindigan sun zama ‘yan ta’adda.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng