Buhari yayi alkawarin kasancewa na kowa amma ya zama na Fulani makiyaya kawai, Gwamnan Benue

Buhari yayi alkawarin kasancewa na kowa amma ya zama na Fulani makiyaya kawai, Gwamnan Benue

- Shugaban kasa yayi alkawarin cewa zai kasance na kowanni dan Nigeria, cewar Ortom

- Gwamnan ya bayyana haka a wani taron manema labarai

- Yace amma shugaban ya kasance kamar na makiyaya ne kawai

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin kasancewa na kowanni dan Nigeria, amma abinda ke nuni kamar shi na Fulani makiyaya ne kawai.

A wani jawabinsa yayin amsar mulki a 2015, Shugaban yayi alkawarin kasancewa "Ni na kowa ne, kuma ba na kowa ba".

A wani tattaunawa da manema labarai a Makurdi ranar Laraba, gwamna Ortom yace babu abinda yake nuni ga shugaban yana jagorancin duk yan Nigeria ne, rahoton The Cable.

Gwamnan ya kara da cewa yan jihar Benue ba bayin fulani bane.

KU KARANTA: Mutum 6 sun ce ga garinku sakamakon gagarumar gobarar kasuwa a Abuja

Buhari yayi alkawarin kasancewa na duk yan Nigeria amma kamar shi na Fulani makiyaya ne kawai- Ortom
Buhari yayi alkawarin kasancewa na duk yan Nigeria amma kamar shi na Fulani makiyaya ne kawai- Ortom Source: The Punch
Asali: Twitter

"Ya Shugaban kasa, idan kana jina, ina so na sanar da kai cewa ka yiwa duk mutanenka yan Nigeria alkawarin adalci , kamar yadda The Punch ta ruwaito yana cewa.

"Kace zaka kasance na kowa ba na kowa ba, amma yanzu yayi nuni cewa kai na fulani ne kawai, saboda babu abinda yake zuwa daga gareka wanda zai sa mutane su ji ajikinsu kai shugabansu ne.

KU KARANTA: Kotu tayi watsi da tuhumar EFCC na badakalar N900bn kan tsohon gwamna Yari

"Kai Shugaban kasan Nigeria ne, ba Shugaban Fulani ba."

"Kai shugaban kowa ne kuma inaso ka sani a matsayinka na mai ruwa da tsaki na wannan kasa, kasani cewa abinda yake faruwa bashi da kyau kuma hakan yana iya sanya rabuwar kai a kasar.

Gwamnan yace ya bukaci gwamnatin tarayya ta yarje lasisin bindigar AK 47 ta yadda yan Nigeria zasu iya kare kansu.

"Shi yasa nayi kira ga gwamnatin tarayya akan ta bani da wasu lasisin rike bindigar AK 47. Saboda idan ina da AK 47, sai ga bafulatani, yasan ina da shi yana dashi, shikenan sai mu fuskanci juna," yace.

"Amma baza ka iya hanani makami kaba bafulatani ba.Wannan ba adalci bane, gwamnatin tarayya tana da san kai. duk rashin tsaron da ake fama dashi gwamnatin tarayya ce ta ja."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel