Mutum 6 sun ce ga garinku sakamakon gagarumar gobarar kasuwa a Abuja

Mutum 6 sun ce ga garinku sakamakon gagarumar gobarar kasuwa a Abuja

- Gagarumar gobara ta tashi a kasuwar tippe da ke Gwarimpa a garin Abuja

- Gobarar ta yi sanadin rasa rayuka shida yayin da wasu suka samu miyagun raunika

- An gano cewa wasu daga cikin 'yan kasuwar suna kwana a shagunansu shiyasa suka mutu

Wata gagarumar gobara ta tashi a kasuwar tippe da ke Gwarinpa a Abuja. An gano cewa mutum 6 sun rasa rayukansu yayin da wasu da yawa suka samu raunika a ranar Alhamis.

Gobarar ta fara ne da daya daga cikin shagunan wanda ya shafa wasu a cikin sa'o'i biyu kafin isowar 'yan kwana-kwana.

Wani ganau ya sanar da The Punch cewa masu kashe gobarar basu iso ba sai wurin karfe 2 na dare bayan kasuwar ta shafe da wuta.

KU KARANTA: Hoton dankareriyar motar miliyoyin naira da Emmanuella ta siya ya janyo cece-kuce

Mutum 6 sun ce ga garinku sakamakon gagarumar gobarar kasuwa a Abuja
Mutum 6 sun ce ga garinku sakamakon gagarumar gobarar kasuwa a Abuja. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

Bata-gari sun yi amfani da wannan damar inda suka dinga balle shaguna suna kwashe kaya kafin isowar masu kashe gobarar.

An samu gawawwaki biyar wadanda aka kai su asibiti yayin da aka samu wata daya da ta kone kurmus.

An ji wani jiyau yana cewa, "An tashe mu wurin karfe 12 na dare. Kusan kowa ya fito ya iso wurin gobarar. Ba mu da yadda za mu yi, haka muka zuba wa sarautar Allah ido.

"Sama da sa'o'i biyu masu kashe gobarar basu iso ba. Mutum shida sun kone kurmus kafin zuwansu. Wasu 'yan kasuwan suna kwana a shagunansu, hakan ce ta sa basu fita ba sai mutuwa.

"Mutane da yawa sun rasa yadda za su yi da rayuwarsu. Hatta gidaje sun kone wadanda ke kusa da nan."

KU KARANTA: Yara 2 sun sheka lahira, mahaifiyarsu ta jigata bayan shan maganin gargajiya a Kano

A wani labari na daban, jam'iyyar APC ta ce bata da shirin tsayar da tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, a matsayin dan takarar jam'iyyar a zaben 2023.

Labarai sun yi ta yawo a makon da ya gabata akan yadda gwamnonin arewa suka tsaya tsayin-daka wurin tabbatar da tsohon shugaban kasan ya samu tikitin.

Sai dai shugaban kwamitin rikon kwarya, Mai Mala Buni ya ce ba gaskiya bane, Daily Trust ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel