Kotu tayi watsi da tuhumar EFCC na badakalar N900bn kan tsohon gwamna Yari

Kotu tayi watsi da tuhumar EFCC na badakalar N900bn kan tsohon gwamna Yari

- Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori karar da a ke kan tsohon gwamnan Zamfara

- Kotun ta bayyana cewa karar da a ka shigar ba a shigar da ita a kan lokacin da ya dace ba

- Kotun ta kori karar tare da nuna cewa irin wannan kara ana shigar da shi ne watanni uku da faruwan lamarin

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Alhamis ta kori karar da ke neman a tilasta wa Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, ta binciki tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, kan zargin karkatar da Naira biliyan 900.

Mai shari'a Okon Abang, a hukuncin da ya yanke, ya yi watsi da karar saboda rashin cancanta.

A baya can wata kungiya, Patriots for the Advancement of Peace and Social Development (PAPS), ta garzaya kotu a wata takardar neman daukaka kara, Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA: 'Yan fasa kwabrin shinkafar waje sun jikkata wasu jami'an Kwastam da wani soja

Kotu tayi watsi da tuhumar EFCC na badakalar N900bn kan tsohon gwamna Yari
Kotu tayi watsi da tuhumar EFCC na badakalar N900bn kan tsohon gwamna Yari Hoto: Premium Times
Asali: UGC

PAPS, ta bakin Shugabanta, Dakta Sani Shinkafi, ya roki kotu da ta umarci EFCC da ta yi aiki da kararraki 15 da ke neman daukar matakin gaggawa daga hukumar ta EFCC.

Mai Shari'a Abang, wanda ya yi watsi da bukatar saboda rashin cancanta, shi ma ya ce an shigar da karar ne ba a kan kari ba.

Alkalin ya ce daidai da umarni na 34 ka'ida ta hudu na Babban Kotun Tarayya, kararraki irin na mai shigar da karan ya kamata a yi su a cikin watanni uku da karbar rahotanni da takaddun da mai shigar da kara ya kafa hujja da su.

Mai shari'a Abang ya ci gaba da cewa bisa ka'idoji, kotun ba ta da hurumin kara lokacin sauraron karar kamar yadda doka ta tanada.

KU KARANTA: NDLEA ta kame wasu 'yan kasuwa 2 dauke da hodar iblis kilogram 3

A wani labarin, Dangantaka mai tsanani tsakanin Kogi da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa / kwamitin shugaban kasa (PTF) akan COVID-19 na kara munana tare da gwamnatin jihar a yanzu da ke barazanar shigar da karar gwamnatin tarayya kotu.

Kingsley Fanwo, Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na Kogi ya bayyana aniyar gwamnatin jihar na kai karar PTF-COVID-19 a Lokoja ranar Laraba kan abin da ya bayyana a matsayin wani yunkurin durkusar da jihar da kuma jefa ‘yan kasa cikin fargaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.