Shugaba Buhari ya umarci IG Adamu ya mika takardar ritayarsa

Shugaba Buhari ya umarci IG Adamu ya mika takardar ritayarsa

- Rahotanni sun bayyana cewa an umarci IG Adamu ya mika takardun barin aiki

- Jita-jitar na nuna da alamun shugaban kasan ya umarce shi ya mika ranar Talata

- Akwai jita-jitan da ke cewa da yiyuwar nada AIG Zanna Ibrahim a matsayin IG

Akwai alamu masu karfi a daren Talata cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Sufeto-Janar na ’Yan sanda Mohammed Adamu ya mika mukaminsa.

Adamu ya kammala aikinsa na shekaru 35 a ranar Litinin, The Nation ta ruwaito.

An sa ran zai mika shi ga babban jami'in da ke bakin aiki a ranar Litinin, amma bai yi hakan ba, yana kara jin cewa za a iya kara masa aiki.

A ranar Talata, Adamu ya kasance a Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe don tarban Shugaba Buhari wanda ya dawo Abuja bayan tafiyar kwanaki hudu zuwa mahaifarsa ta Daura.

An gano cewa an fada wa IG makomar sa bayan isowar Shugaba Buhari.

KU KARANTA: Hanya mafi sauki don magance rikicin makiyaya, Mataimakin gwamnan Benue

Shugaba Buhari ya umarci IG Adamu ya mika takardar ritayarsa
Shugaba Buhari ya umarci IG Adamu ya mika takardar ritayarsa Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Wata majiya mai tushe ta ce: “Shugaban kasa ya nemi IGP ya mika mukaminsa.

“Adamu yana jiran umarnin shugaban kasa. Da zai tafi a ranar Litinin amma zai zama ba zai yuwu ba da ya fita ba tare da cikakken umarnin Shugaban kasa da Babban Kwamanda ba.

“Wataƙila zai iya miƙa shi ga babban mataimakin babban sufeto-janar na 'yan sanda. Ina sane da cewa Adamu ya kasance a jiya yana sanya takardun mikawa.”

Akwai jita-jita a ranar Talata cewa ana iya nada AIG Zanna Ibrahim a matsayin IGP.

An gano cewa an yi shagali a Kwalejin 'Yan sanda ta Najeriya da ke Wudil, Jihar Kano, ranar Talata da wasu jami'an kwalejin suka yi.

“Shi masani ne, muna ta murna tun lokacin da muka ji labarin yiwuwar zabanshi.

"Ba mu gan shi ba amma mataimakinsa ya zo ofishinsa da yammacin yau don share wasu abubuwa daga teburinsa," in ji wani malami.

KU KARANTA: Kwalejin kimiyya da fasaha na Adamawa za ta fara karatun digiri, in ji Rector

A wani labarin, Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu ya isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja a ranar Talata lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa Katsina.

Ya kamata Adamu ya sauka daga kujerarsa a ranar Litinin, saboda cikarsa shekaru 60, The Cable ta wallafa.

A ranar Talata ne aka ga IGP din ya je tarbar Buhari yayin dawowarsa daga tafiyar da yayi zuwa Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel