Fadar Shugaban kasa ta bankado wani shiri da ake yi na batawa Buhari suna a Jaridu da kafafen yada labarai

Fadar Shugaban kasa ta bankado wani shiri da ake yi na batawa Buhari suna a Jaridu da kafafen yada labarai

- Bayan mayar da martani kan rahoton rashawa, fadar shugaban kasa ta ce ana kokarin batawa Buhari suna

- Wannan karon, fadar shugaban kasa na zargin za'a yi amfani da kafafen yada labarai

Fadar Shugaban kasa a ranar Juma'a 29 ga watan janairun 2012 tace ta bankado wani shiri da ake yi na batawa shugaban kasa Muhammadu Buhari suna saboda a bata mai martabarsa.

A bisa wani jawabi da mai ba Shugaban kasa shawara a kafafen watsa labarai, Femi Adesina ya saki a kafar sada zumuntar facebook, yace akwai wani hari da ake yi na nuna cewa Shugaban kasa yana nuna banbancin kabila, kuma hakan yaci karo akan abinda yayi alkawari akai na cewa duk yan Nigeria daya suke.

Legit.ng ta rahoto muku cewa a watan Disamba 2020, Adesina ya bayyana cewa akwai wani shiri da akeyi wanda ke nuni da cewa Shugaban kasa ba shi yake tafiyar da al'amuran gwamnati ba.

Adesina ya kara da cewa shirin zaizo da wasu labarai na cewa Shugaban kasan yana amfani da karfin mulki wajen ganin cewa ya kare wata kabila daga laifuka.

Hadimin Shugaban kasan ya kara da cewa duk ana shirin haka ne dan a kawo tashin hankali da fargaba a kasar.

Yace duk wadannan labarai marasa tushe zasu yi nuni da cewa Shugaban yana ba yan kabilar shi manyan mukamai a gwamnati.

KU KARANTA: An yi bikin karrama Buratai bisa namijin kokarin da ya yiwa Najeriya (Hotuna)

Fadar Shugaban kasa ta bankado wani shiri da ake yi na batawa Buhari suna a Jaridu da kafafen yada labarai
Fadar Shugaban kasa ta bankado wani shiri da ake yi na batawa Buhari suna a Jaridu da kafafen yada labarai Hoto: Presidency
Asali: Twitter

DUBA NAN: Sauran yan Najeriya sama da 400 da suka makale a Saudiyya sun dawo gida

A baya kunji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci yan Nigeia dasu nisanta kansu akan duk abinda zai kawo rabuwar kai a kasar.

Shugaban ya bayyana hakane a rana Alhamis 28 ga watan Janairu, yayinda kungiyar NSCIA ta kai mai ziyara a fadarshi da ke Aso Villa.

A bangare guda, shugaba Muhammadu Buhari ya tashi da Abuja inda ya nufi Daura, jihar Katsina, mahaifarsa domin musharaka a sabon rijistan mambobin jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Buhari ya tashi daga Abuja ne bayan halartan Sallar Juma'a a Masallacin fadar shugaban kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel