Da duminsa: Sauran yan Najeriya sama da 400 da suka makale a Saudiyya sun dawo gida

Da duminsa: Sauran yan Najeriya sama da 400 da suka makale a Saudiyya sun dawo gida

- Bayan kuka da suka kaiwa gwamnatin Najeriya, an dawo da mata da maza sama da 800 Najeriya daga saudiyya

- An tsaresu a can bisa zargin zama a kasar ba bisa ka'ida ba

Sauran yan Najeriya 419 da suka makale a kasar Saudiyya sun dawo ranar Juma'a 29 ga Junairu, bayan sahun farkon mutane 384 da suka dawo ranar Alhamis.

Wadanda suka dawo sun hada da maza 126 da mata 293, da yara, kuma sun dira a tashar jirgin saman Nnamdi Azikwe cikin jirgi mai lamba SV-3413 misalin karfe 11:57 na safe.

Hukumomi sun ce za'a killacesu na tsawon wani lokaci kafin a mayar da su jihohinsu.

A jiya, yan Najeriya 384 cikin 802 da suka yi kuka ga gwamnatin Najeriya ta cecesu daga kasar Saudiyya inda suka makale sun dira gida Najeriya ranar Alhamis, 28 ga Junairu, 2021.

An tsare su a wurare daban-daban da ake tsare mutane a Saudiyya kan batun kaura ba bisa ka'ida ba.

Sakataren din-din-din na Ma’aikatar Harkokin Waje, Gabriel Aduda, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce za a karbi wadanda za su dawo din ne a Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, ta hanyar jiragen sama biyu na Saudiyya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel