An yi bikin karrama Buratai bisa namijin kokarin da ya yiwa Najeriya (Hotuna)
- Laftanan Janr Tukur Yusuf Burati ya yi murabus a aikin Soja bayan shekaru 40
- Attahiru ya karba ragamar mulki daga hannun Janar Tukur Buratai ranar Alhamis
- Laftanan Janar Tukur Yusuf Burati ya yi murabus a aikin Soja bayan shekaru 40
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Juma'a ya halarci bikin karrama tsohon shugaban hafsoshin sojin kasa, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai, da aka gudanar a Abuja.
An yi bikin faretin ne a Mogadishu Cantonment dake Asokoro, wanda akafi sani da Abacha Barracks.
Bikin wani al'ada ne a gidan Soja domin karrama hafsoshin da suka yi ritaya bisa bautar da suka yiwa kasa.
Daga cikin wadanda suka halarci bikin akwai Sarkin Biu, Mai Mustapha Umar Mustapha II, Sanata Ali Ndume, da kwamishanan shari'ar jihar Borno, Kaka Shehu Lawan.
Kalli hotunan:
KU KARANTA: Bayan shekaru biyar, an ceto daya daga cikin yan matan Chibok
KU KARANTA: Wadanda Buhari ya naɗa manyan hafsoshin sojoji sun cancanta, in ji Shettima
A jiya mun kawo muku cewa, an yi taron mika mulki daga hannun wanda ya sauka daga karagar zuwa sabon da shugaban kasa ya nada, a ranar Alhamis, 28 ga watan Junairu, 2021.
A wannan taro mai kayatarwa da aka gudanar a farfajiyar taron hedkwatar sojin kasa dake birnin tarayya Abuja, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai, ya mika tutan fara aiki ga sabon shugaban hafsan Sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami dukkan hafsoshin tsaron Najeriya a ranar Talata, 26 ga watan Junairu, 2021, kuma ya nada sabbi ba tare da bata lokaci ba.
Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng