Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya sake shillawa Daura, jihar Katsina
- Shugaba Buhari ya yi tafiyarsa na farko tun da aka shiga sabon shekara
- Jam'iyyar APC za ta fara shirin sake rijistan mambobinta a fadin tarayya
- Buhari zai koma birnin tarayya bayan kwanaki hudu a jihar Katsina
Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi da Abuja inda ya nufi Daura, jihar Katsina, mahaifarsa domin musharaka a sabon rijistan mambobin jam'iyyar All Progressives Congress, APC.
Buhari ya tashi daga Abuja ne bayan halartan Sallar Juma'a a Masallacin fadar shugaban kasa.
Mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaba Buhari zai kwashe kwanaki uku a Daura kafin komawa birnin tarayya.
Gabanin tafiyarsa, ya karbi bakuncin gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, wanda ya bayyanawa manema labarai cewa ya tattauna lamarin tsaro da kasuwar Jos ne da shugaban kasan.
A ranar Asabar, ana sa ran shugaba Buhari zai je gundumarsa ra Sarkin Yara domin rijista matsayin mamban jam'iyyar.
DUBA NAN: An yi bikin karrama Buratai bisa namijin kokarin da ya yiwa Najeriya (Hotuna)
KU KARANTA: Sauran yan Najeriya sama da 400 da suka makale a Saudiyya sun dawo gida
A bangare guda, shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Michika, jihar Adamawa da wasu mambobin jam'iyyar 5000 sun sauya sheka jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Mista John Fave wanda ya jagoranci masu sauya shekar ya ce sun koma PDP ne domn taimakawa jam'iyyar, Jaridar Leadership ta ruwaito.
Shugabannin jam'iyyar sun hada shugaban APC na karamar hukumar, tsohon dan majalisar wakilai, Mista James Ijai, da wasu shugabannin jam'iyyar a gunduma-gunduma 10.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng