Yanzu-yanzu: Buhari yana ganawa da Sarkin Musulmi da sauran mambobin NSCIA

Yanzu-yanzu: Buhari yana ganawa da Sarkin Musulmi da sauran mambobin NSCIA

- Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga taro da Sarkin Musulmi a gidan gwamnati a Abuja

- Sarkin musulmin ya yi wa sauran mambobin kwamitin kolin musulunci, NSCIA, jagoranci zuwa taron

- Wasu daga cikin yan fadar shugaban kasa da suka hada da ministoci da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa sun hallarci taron

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana ganawa da mambobin kwamitin kolin harkokin addinin musulunci ta Najeriya, NSCIA.

Ana gudanar da taron ne a gidan gwamnati na Aso Rock Villa da ke Abuja.

Shugaban NSCIA kuma Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa'ad Abubakar ne ya jagoranci mambobin na NSCIA zuwa wurin taron.

DUBA WANNAN: Shekau ya fitar da sabon sautin murya, ya gargadi sabbin shugabanin sojoji da Buhari ya naɗa

Yanzu-yanzu: Buhari yana ganawa da Sarkin Musulmi da sauran mambobin NSCIA
Yanzu-yanzu: Buhari yana ganawa da Sarkin Musulmi da sauran mambobin NSCIA. Hoto: @BashirAhmaad
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kuɗin ɗawainiyar jana'izar mahaifina na ke nema, matashin da aka kama da katin ATM 17

A halin yanzu ba a bayyana dalilin taron ba ko abinda suke tattaunawa ba.

Cikin wadanda suka hallarci taron kawai Etsu Nupe, Yahaya Abubakar, ministan Abuja, Mohammed Bello, ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ministan labarai da al'adu, Mista Lai Mohammed.

Saura sun hada da mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, NSA, Manjo Janar Babagana Mongunu da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa , Farfesa Ibrahim Gambari.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel