Kuɗin ɗawainiyar jana'izar mahaifina na ke nema, matashin da aka kama da katin ATM 17

Kuɗin ɗawainiyar jana'izar mahaifina na ke nema, matashin da aka kama da katin ATM 17

- An kama wani matashi mai shekara 37 da ake zargin dan damfara ne da katinan cirar kudi ATM 17

- Matashin wanda ya alakanta laifin da sharrin shaidan ya ce ya shiga harkar ne don ya tara kudin da zai binne mahaifin shi

- Rundunar yan sandan Jihar Edo ta bayyana cewa matashin ya yi nasarar cirar ₦40,000 da kuma ₦55,000 daga katinan mutane biyu kafin a kai ga kama shi.

Wani dan shekara 37 da ake wa zargin damfara, Kelvin Odion, ya shiga komar yan sanda a Jihar Ogun bayan ya mallaki katinan ATM 17 ba bisa ka'ida ba, The Punch ta ruwaito.

Odion, wanda ya yi ikirarin shi dan asalin Jihar Edo ne, an kama shi ranar 21 ga watan Janairu lokacin da ya kai wa dan uwan sa ziyara a Ijebu-Ode.

Kuɗin ɗawainiyar jana'izar mahaifina na ke nema, matashin da aka kama da ATM 17
Kuɗin ɗawainiyar jana'izar mahaifina na ke nema, matashin da aka kama da ATM 17. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An girke sojoji mata 300 a hanyar Kaduna zuwa Abuja don maganin masu garkuwa

An yi bajin kolin sa tare da wasu mutane 49 da ake zargi da laifuka daban daban a hedikwatar yan sanda, Eleweran, ranar Laraba.

Kwamishinan yan sandan Jihar, Edward Ajogun, ya ce DPO din Igbeba ya samu kiran wayar da ke sanar da shi game da barayin ATM.

Ya ce Odion ya samu nasarar amfani da katinan ATM tare da cire ₦40,000 da kuma ₦55,000 daga cikin katinan mutane biyu, kafin a kama shi.

KU KARANTA: Zulum ya yi maraba da naɗin sabbin manyan hafsoshin sojoji da Buhari ya yi

Da yake zantawa da manema labarai, Odion, wanda ya alakanta laifin na sa da sharrin shaidan, ya ce ya shiga laifin ne lokacin da ya ke neman kudin da zai binne mahaifin sa.

Ya ce, "hudu daga cikin katinan na shi ne; akwai na mata ta ma. Wasu kuma tsintar su nayi.

"Na fara cikin watan Disamba lokacin da mahaifina ya rasu. Ina neman kudin da zan binne shi ne. Baba na ya rasu 15 ga Disamba ni kuma na fara 20 ga Disamba. Ina bukatar kudaden da zan biya dakin ajiyar gawa. Na samu ₦95,000 daga cikin ₦200,000.

"Ni dan kasuwa ne, ina siyar da takalma a Lagos. An kama ni lokacin da na kawo wa dan uwa na ziyara a Ijebu-Ode. Nayi nadamar abin da na aikata. Sharrin shaidan ne."

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164