Shekau ya fitar da sabon sautin murya, ya gargadi sabbin shugabanin sojoji da Buhari ya naɗa

Shekau ya fitar da sabon sautin murya, ya gargadi sabbin shugabanin sojoji da Buhari ya naɗa

- Shugaban tsagi guda na kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da sabon sako game da sabbin manyan hafsoshin tsaro

- A sakon mai tsawon kimanin mintuna 9, Shekau ya shaidawa sabbin shugabannin sojojin cewa babu wani abu da za su iya yi da magabatansu ba su yi ba

- Bayan ambaton sunayensu da ayyukansu, Abubakar Shekau ya yi kira gare su da su tuba su rungumi musulunci

Abubakar Shekau, shugaban tsagi guda na kungiyar Boko Haram ya fitar da sabon sautin murya inda ya yi magana game da nadin sabbin manyan hafsoshin Najeriya, inda ya ce babu wani abu da za su iya tabukawa da magabatansu ba su yi ba a yaki da ta'addanci a arewa maso gabas, HumAgle ta ruwaito.

A sautin da ya fitar mai tsawon mintuna tara da dakika 56, Shekau ya ce ya ji labarin yi wa tsaffin manyan hafsoshin tsaron murabus da maye gurbinsu da sabbi amma ya yi kira garesu su amshi musulunci.

'Ba za ku iya yin wani abu da magabatanku ba su yi ba': Shekau ga sabbin manyan hafsoshin sojoji
'Ba za ku iya yin wani abu da magabatanku ba su yi ba': Shekau ga sabbin manyan hafsoshin sojoji. Hoto: Hum Angle
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kuɗin ɗawainiyar jana'izar mahaifina na ke nema, matashin da aka kama da katin ATM 17

A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da yi wa tsaffin manyan hafsoshin tsaron murabus tare da maye gurbinsu da sabbi.

Kungiyoy da mutane da dama sun dade suna kira da shugaban kasar ya sauya manyan hafsoshin tsaron.

A cikin sabon sautin muryar da Shekau ya fitar, ya ambaci sunayen manyan hafsohin tsaron daya bayan daya da ayyukansu sannan ya yi kira garesu da su tuba domin babu wani abu da za su iya yi domin tarwatsa kungiyarsa.

KU KARANTA: An girke sojoji mata 300 a hanyar Kaduna zuwa Abuja don maganin masu garkuwa

"Leo Irabor, shugaban sojoji, ka tausayawa kanka, ka tuba ka amshi musulunci. Babu abinda zaka iya yi," in ji Shekau.

Ya ce Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya dena rudar kansa domin shi musulmi ne.

"Ko da kai musulmi ne amma kana yin shirka, yanzu kai ba musulmi bane," in ji Shekau.

Wata majiya da ke da masaniya kan ayyukan Boko Haram ta shaidawa HumAngle cewa akwai yiwuwar kungiyar na shirya kai babban hari don ya zama ishara ga sabbin manyan hafsoshin tsaron cewa ba za su saduda ba.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164