Ngige ya yi murnar sallamar manyan hafsoshin sojoji, ya yabawa Buhari kan naɗa sabbi

Ngige ya yi murnar sallamar manyan hafsoshin sojoji, ya yabawa Buhari kan naɗa sabbi

- Sanata Chris Ngige, ministan kwadago da ayyuka ya taya Shugaba Buhari murna bisa nadin sabbin manyan hafsoshin sojoji

- Ngige ya bayyana sauyan manyan hafsoshin tsaron a matsayin goron sabon shekara da Buhari ya bawa yan Najeriya

- MInistan ya kuma ce yan kabilar Ibo sun yi murna domin nada Janar Leo Irabor wanda ya fito daga Niger Delta hakan kuma na nuna shugaban kasa baya kabilanci

Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige ya taya Shugaba Muhammadu Buhari murna saboda nada sabbin manyan hafsoshin sojoji inda ya bayyana shi a matsayin "cika alkawari", Premium Times ta ruwaito.

Sanarwar da ta fito daga sashin watsa labarai na Sanata Chris Ngige a Abuja ta ce nadin "goron sabuwar shekara ne ga 'yan Najeriya' kuma ya yaba wa shugaban kasar saboda sauraron kiraye-kirayen yan Najeriya."

Ngige ya yi murnar sallamar manyan hafsoshin sojoji, ya yabawa Buhari kan nada sabbi
Ngige ya yi murnar sallamar manyan hafsoshin sojoji, ya yabawa Buhari kan nada sabbi. @PremiumTimesNG
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kungiyar tsaffin dalibai na MSS sun nuna kin amincewarsu kan yunkurin rushe masallacin makaranta a Binuwai

"Duk da cewa wasu ba su sani ba, shugaban kasa ya fada wa wasu tsirarun yan Najeriya cewa zai nada sabbin manyan hafsoshin tsaro a sabuwar shekarar. Ya cika alkawarinsa kuma babu shakka shugaba ne mai sauraron al'umma."

Har wa yau sanarwar ta ce nadin ya yi wa yan kabilar Ibo dadi domin sabon shugaban hafsoshin tsaro, Janar Leo Irabor dan asalin karamar hukumar Ika ta Kudu ne daga jihar Delta kuma dan yankin Niger Delta don haka wannan alama ce da ke nuna shugaban kasar baya nuna kabilanci.

KU KARANTA: 'Jami'an tsaro na IPOB sun halaka Hausawa 4 a Imo'

"Nadin ya nuna karara cewa shugaban kasa yana la'akari da cancanta ne kuma ya kan zabo tawagarsa daga bisa cancanta daga kowanne yanki na kasar."

Idan za a iya tunawa Mista Ngige yayin da ya wakilci Shugaba Buhari a wurin jana'izar Bishop Gregory Ochiagha a ranar Litinin 11 ga watan Janairun 2021 ya shaidawa al'umma cewa shugaban kasa ya yi alkawarin yi wa hukumomin tsaro garambawul a sabon shekara.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel