Kungiyar tsaffin dalibai na MSS sun nuna kin amincewarsu kan yunkurin rushe masallacin makaranta a Binuwai

Kungiyar tsaffin dalibai na MSS sun nuna kin amincewarsu kan yunkurin rushe masallacin makaranta a Binuwai

- Kungiyar MSS din tsofaffin daliban GSS, Otukpo ta bi ba'asin yunkurin rushe masallaci a harabar makantar

- Kungiyar wadda bata dade da kamalla gyara masallacin ba ta ce a dakata da yunkurin rushe masallacin mai shekara fiye da 40

- Gwamnatin Jihar Benue ta bakin ma'aikatar ilimi ta ce tuni aka shawo kan wannan batu

Kungiyar dalibai musulmi (MSS) na tsofaffin daliban Government Secondary School (GSS), Otukpo, Jihar Benue, sun bi ba'asin yunkurin rushe wani masallaci da ke harabar makarantar, Daily Trust ta ruwaito.

Amma, gwamnatin jihar ta bakin ma'aikatar ilimi ranar Talata, tayi ikirarin an shawo kan wannan batu.

Kungiyar MSS ta nuna kin amincewarta kan yunkurin rushe masallaci a Binuwai
Kungiyar MSS ta nuna kin amincewarta kan yunkurin rushe masallaci a Binuwai. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da dumi-dumi: Buhari ya naɗa Aghughu a matsayin sabon AGF

A wata takarda da aka aike wa Kwamishinan ilimi na jihar, Prof. Dennis Ityavyar, kungiyar ta ce hukumar tsare birane da ci gaba (UDB) ranar 20 ga Janairu, 2021, tayi wa masallacin wanda ita (MSS) ba ta dade da gyara shi ba za a rushe.

Yan kungiyar MSS kuma tsofaffin daliban GSS, Otukpo, mun yi rubuta don jin ba'asin rushe masallacin makaranta.

"Muna kira ga kwamishina da a dakata da yunkurin karkata ba mu dade da yi masa kwaskwarima ba a GSS, Otukpo, a kuma dawo da shugaban makarantar saboda idan ka cire wa yarje mana da aka yi don gyara masallacin, ba a ba shi ko kobo ko an tuntube shi don bashi kwangila ba," kamar yadda kungiyar ta shaida

KU KARANTA: Sojoji sun sada ƴan Boko Haram 8 da mahallacinsu bayan musayar wuta a Borno da Yobe

Sun kuma bayyana cewa an gina masallacin shekaru 42 da suka gabata, su na masu cewa, "duba da yadda masallacin ya lalace, mu, tsofaffin daliban makarantar GSS, Otukpo, kungiyar MSS muka bukaci zamu gyara masallacin."

A na shi bangaren, shugaban UDB, Dr Saint Gbilekaa, ya ce ya samu kwafin korafin su a ofishin sa.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: