Wadanda suka kona min gida zasu haukace cikin kwana 2, Sunday Igboho

Wadanda suka kona min gida zasu haukace cikin kwana 2, Sunday Igboho

- Sunday Igboho ya lashi takobin korar Fulani Makiyaya daga jihar Oyo da sauran jihohin kudu maso yamma

- Daren Litinin, wasu yan bindiga sun bankawa gidansa wuta

- Igboho ya lashe takobin daukar fansa kan abin da akayi masa

Mai rajin kafa kasar Oduduwa, kuma mutumin da ya lashi takobin korar Fulani daga kasar Yarbawa, Sunday Igboho, ya bayyana cewa wadanda suka kona masa gida zasu haukace cikin sa'o'i 48.

Igboho a shafinsa na Tuwita ya bayyana hotunan gidansa da ya kone yana mai cewa: "Misalin karfe 1 na dare wannan ya faru."

"Sun dauka ina gidan ne. Ina nan cikin koshin lafiya da mutane na. Ba zaku iya kashe iska ba. Cikin awanni 48hrs za'a bayyana wadanda suka yi harin kuma zasu haukace."

Wadanda suka kona min gida zasu haukace cikin kwana 2, Sunday Igboho
Wadanda suka kona min gida zasu haukace cikin kwana 2, Sunday Igboho
Asali: UGC

DUBA NAN:Likitoci 3 sun mutu, 53 suna fama da Covid-19 a Kano

A bangare guda, hukumar yan sandan jihar Oyo ta tabbatar da labarin cewa wasu yan bindiga cike da motar bas da tasi sun banka wuta gidan mutumin da ya ke kokarin korar Fulani daga kasar Yarbawa, Sunday Igboho.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata, Punch ta ruwaito.

Fadeyi ya ce an bayyanawa yan sanda cewa sai da yan bindigan suka yi harbe-harbe sama kafin suka bankawa gidan wuta dake unguwar Soka, Ibadan.

Ya ce yan sandan sun kaddamar da bincike kan lamarin.

An bayyana cewa an kona gidan ne misalin karfe 3 na dare bayan dauke wuta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel