Yan sanda sun tabbatar da kona gidan Igboho, sun ce yan bindiga ne

Yan sanda sun tabbatar da kona gidan Igboho, sun ce yan bindiga ne

- An waye gari da labarin cewa wasu sun kai hari gidan Sunday Igboho

- Kakakin hukumar yan sanda ta saki jawabi kan hakan

Hukumar yan sandan jihar Oyo ta ce ta samu labarin cewa wasu yan bindiga cike da motar bas da tasi sun banka wuta gidan mutumin da ya ke kokarin korar Fulani daga kasar Yarbawa, Sunday Igboho.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata, Punch ta ruwaito.

Fadeyi ya ce an bayyanawa yan sanda cewa sai da yan bindigan suka yi harbe-harbe sama kafin suka bankawa gidan wuta dake unguwar Soka, Ibadan.

Ya ce yan sandan sun kaddamar da bincike kan lamarin.

An bayyana cewa an kona gidan ne misalin karfe 3 na dare bayan dauke wuta.

Jawabin yan sanda yace: "Misalin karfe 0620 hrs na yau 26/01/2021, wani rahoto da ofishin yan sandan Santo ta samu shine wasu yan bindiga sun je gidan Sunday Igboho dake unguwar Soka na Ibadan cikin mota kirar Hummer bas da Micra suna harbi, kuma suka bankawa gidan wuta."

"An kona karamin dakin da kuma dukiyoyin dake ciki."

"Daga baya an kashe wutan. Hakazalika an kaddamar da bincike kan lamarin yayinda yan sanda ke kan bibiyan yan bindigan."

KU DUBA: Kaiwa Fulani hari a kasar Yarabawa na iya haddasa wani yakin basasa

Yan sanda sun tabbatar kona gidan Igboho, sun ce yan bindiga ne
Yan sanda sun tabbatar kona gidan Igboho, sun ce yan bindiga ne
Source: UGC

KU KARANTA: Sifeto Janar na yan sanda ya bada umurnin kama mutumin da ya kori Fulani a Oyo

A bangare guda, Sunday Igboho, ya bayyana cewa wadanda suka kona masa gida zasu haukace cikin sa'o'i 48.

Igboho a shafinsa na Tuwita ya bayyana hotunan gidansa da ya kone yana mai cewa: "Misalin karfe 1 na dare wannan ya faru."

"Sun dauka ina gidan ne. Ina nan cikin koshin lafiya da mutane na. Ba zaku iya kashe iska ba. Cikin awanni 48hrs za'a bayyana wadanda suka yi harin kuma zasu haukace."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel