Korona ta yi tsanani: Kimanin mutane 2400 sun kamu jiya, mafi yawa tun da cutar ta bulla

Korona ta yi tsanani: Kimanin mutane 2400 sun kamu jiya, mafi yawa tun da cutar ta bulla

- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara

- Sama da makonni biyu a jere, yan Najeriya sama da 1000 ke kamuwa da Korona kullum

- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar hana fita idan adadin ya cigaba da karuwa

Mutane 2,314 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Juma'a, 22 ga watan Junairu 2021, kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 118,969 a Najeriya.

Daga cikin mutanen da suka kamu, an sallami 94,877 yayinda 1497 suka rigamu gidan gaskiya.

Ga jerin wadanda suka kamu a jihohi ranar Litinin:

Lagos-831

Kaduna-545

FCT-235

Plateau-127

Nasarawa-80

Oyo-72

Delta-65

Rivers-64

Kano-46

Ogun-46

Bayelsa-30

Gombe-30

Abia-28

Osun-27

Edo-25

Ondo-14

Sokoto-12

Zamfara-10

Bauchi-8

Imo-5

Jigawa-4

Ekiti-4

Borno-4

Niger-2

DUBA NAN: Za mu fara yiwa duk mai son shiga Kano gwajin Korona, Ganduje

Korona ta yi tsanani: Kimanin mutane 2400 sun kamu jiya, mafi yawa tun da cutar ta bulla
Korona ta yi tsanani: Kimanin mutane 2400 sun kamu jiya, mafi yawa tun da cutar ta bulla Credit: @NCDCgov
Asali: Twitter

KU DUBA: COVID-19: Ba zamu kulle makarantun jihar Kano ba, gwamna Ganduje

A bangare guda, Shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana cewa amfanin barin yara su koma makaranta ya rinjayi tsoron kamuwa da cutar Korona.

Ihekweazu ya bayyana hakan a taron kungiyar likitocin yaran Najeriya watau (PAN) ranar Juma'a a jihar Legas, The Cable ta ruwaito.

Ihekweazu ya ce lallai ya yi na'am da shawaran bude makarantu.

Diraktan ya ce Najeriya ta fi kowace kasa yawan adadin yara maras zuwa makaranta a duniya, kuma cigaba da ajiyesu a gida babban illa ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel