Muna sa ran alaka ta kwarai da gwamnatinka, Buhari ga Joe Biden

Muna sa ran alaka ta kwarai da gwamnatinka, Buhari ga Joe Biden

- Shugaba Buhari ya taya Joe Biden murnar rantsar da shi matsayin shugaban Amurka

- Biden ya zama shugaban kasar Amurka na 46

- Buhari ya yi alaka na kwarai tsakaninsa da tsohon shugaba Donald Trump

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, ya ce gwamnatinsa na kyautata zaton alaka ta kwarai da gwamnatin sabon shugaban Amurka, Joe Biden.

A jawabin da mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu, ya sace mai taken "Shugaba Buhari: Muna sa ran aiki da shugaba Joe Biden da mataimakiyar shugabansa Kamala Harris", Buhari ya ce yana kyautata karfafa alaka da hadin kai da kuma goyon baya ga Najeriya da Afirka.

Shugaba Buhari ya taya sabon shugaban kasan da al'ummar Amurka murnan hawa karagar mulki.

Yace: "Muna kyautata zaton karfafa alakarmu da mutunci da gwamnatin Biden, wajen yaki da ta'addanci, canjin yanayi, talauci, da inganta tattalin arziki."

"Muna fatan cewa wannan lokaci zai kawo abubuwa masu kyau tsakanin kasashenmu biyu, yayinda muke fuskantar abubuwan da suka shafemu."

Buhari ya taya Amurka alfaharin samun mace ta farko da zata rike matsayin mataimakin shugaban kasa kuma mai asali daga Afrika da Asiya.

KU DUBA: Abubuwan da Trump ya fadawa Magoya bayansa da ya bar fadar White House

Muna sa ran alaka ta kwarai da gwamnatinka, Buhari ga Joe Biden
Muna sa ran alaka ta kwarai da gwamnatinka, Buhari ga Joe Biden
Source: Twitter

KU KARANTA: Abubuwan da Trump ya fadawa Magoya bayansa da ya bar fadar White House

Dazu kun ji cewa an rantsar Joe Biden a matsayin shugaban kasar Amurka na 46 a ranar Laraba, 20 ga watan Junairu, 2021, a harabar majalisar dokokin kasar, Capitol.

Hakazalika an rantsar da abokiyar tafiyarsa na zaben ranar 3 ga Nuwamba, 2020, Kamala Harris.

Shugaban Alkalan Amurka, CJ John Roberts ne ya rantsar da shugaban.

Joe Biden wanda ke da shekara 78 da haihuwa ya zama shugaban Amurka mafi shekaru a tarihi, yayinda mataimakiyarsa, Kamala Harris, ta zama macen farko da ta zama mataimakiyar shugaban kasa a tarihin kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel