Abubuwan da Trump ya fadawa Magoya bayansa da ya bar fadar White House

Abubuwan da Trump ya fadawa Magoya bayansa da ya bar fadar White House

- Donald Trump ya gabatar da jawabinsa na karshe daga Maryland dazu

- Shugaban Amurkan mai barin-gado ya furta cewa ‘muna nan dawowa’

- Trump bai kira sunan Biden ba, amma ya yi masa fatan alheri a jawabin

Donald Trump ya yi wa jama’a jawabi kafin jirgin sama ya dauke shi zuwa mahaifarsa, Florida.

Babu wata takarda a gaban Trump a lokacin da ya ke magana, inda ya yi kira ga jama’a: “A bi a hankali matuka’ game da ‘mummunar; annobar COVID-19.”

Shugaban kasar mai barin-gado ya yi jawabi ne a filin sojoji da ke Maryland, bayan ya tattara ya bar fadar shugaban kasa tare da mai dakinsa, Melania Trump.

BBC ta rahoto shugaban mai barin-gado ya na fada wa magoya baya cewa zasu dawo. Ana ganin wannan magana tana iya daukar fassara da ma’ana iri-iri.

KU KARANTA: Za a rantsar da Joe Biden a kan mulki, Donald Trump ya tattara ya bar fada

A gajeren jawabin Donald Trump, ya ce “Zamu dawo a wani irin yanayi”. Bisa dukkan alamu har yanzu Trump bai yarda ya sha kashi a zaben da aka yi ba.

Babu wata takarda a gaban Trump a lokacin da ya ke magana, inda ya yi kira ga jama’a: “A bi a hankali matuka’ game da ‘mummunar; annobar COVID-19.”

“Ina mai matukar alfaharin zama shugaban kasarku.” Inji Trump kafin jirginsa ya tashi, ya na kuri da samar da dinbin ayyukan yi ga mutanen Amurka.

Ko da Trump bai halarci bikin rantsar da magajinsa ba, ya yi masa fatan alheri. Ya ce: “Ina yi wa sabuwar gwamnati fatan gagarumar nasara da gagarumar sa’a.”

Abubuwan da Trump ya fadawa Magoya bayansa karshe da ya bar fadar White House
Donald J. Trump Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Biden ya karya tarihin da Trump ya kafa a Kasar Amurka a 2017

“Zan cigaba da yi maku yaki. Ina kallo, ina sauraro.” Ya kara da cewa: “Ina tunanin (Biden) za su samu nasara sosai. Sun samu tubulin yin abin burgewa.”

Trump ya gode wa iyalinsa, abokai da ma’aikatan da suka taimaka masa a shekaru hudu. A cewarsa gwamnatinsa tayi namijin kokari, ya ambaci nasarorinsa.

A yau Laraba, 20 ga watan Junairu, 2021, Donald Trump ya bar kujerar shugaba Amurka, inda aka rantsar da Joe Biden a matsayin sabon shugaban kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng