Tarihi 5 da za a kafa yayin da Joe Biden ya hau kujerar Shugaban kasa a Amurka

Tarihi 5 da za a kafa yayin da Joe Biden ya hau kujerar Shugaban kasa a Amurka

- Joe Biden ya dare kujerar shugaban Amurka yana ‘Dan shekara 78 a Duniya

- Mataimakiyarsa ce bakar fata kuma macen farko da ta samu wannan mukami

- Donald Trump ya bar ofis ya na da shekara 77 – ya kusa karya tarihin Reagan

A yau 20 ga watan Junairu, 2021, aka rantsar da Joe Biden da Kamala Harris a matsayin shugaban kasa da mataimakiyar shugabar kasar Amurka.

A wannan rana, abubuwan da suka faru sun bar tarihi a siyasar Amurka. Legit.ng Hausa ta tattaro maku kadan daga cikin tarihin nan da aka kafa.

1. Rashin halartar shugaba mai barin-gado wajen rantsuwa

Donald Trump wanda ya bar kan mulki, ya zama shugaban Amurka na farko a shekaru 47 da ya ki halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasa.

KU KARANTA: Joe Biden mai jiran-gado ya dura Washington, Trump ya yi gaba abinsa

Rabon da ayi wannan tun lokacin Richard Nixon wanda ya yi murabus, ya bar Gerald Ford a 1974.

2. Mace ta zama Mataimakiyar shugaban kasa

A karon farko a tarihin Amurka, an samu macen da ta rike kujerar mataimakiyar shugaban kasa, shekaru 100 bayan an ba mata damar su fito su yi zabe.

3. Bakar fata ta rike Mataimakiyar shugaban kasa

Haka zalika Kamala Harris ce bakar fatar farko da ta hau kujerar mataimakiyar shugaban kasa. Kuma ita ce mai jinin Nahiyar Asiyar farko a mukamin.

Mahaifiyar Harris mutumiyar Indiya ce, an kuma haifi mahaifinta a kasar Jamaica kafin su tare a Oakland.

4. Tsohon shugaban kasa

Joe Biden ya karya tarihin Donald Trump na zama shugaban kasar Amurka da ya fi tsufa. Biden ya gaji Trump ya na da shekara 78 da watanni biyu a Duniya.

Tarihi X da za a kafa yayin da Joe Biden ya hau kujerar Shugaban kasa a Amurka
Kamala Harris ta zama #2 a kasar Amurka Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Donald Trump ya tattara inasa-inasa daga fadar White House

5. Tsohon shugaba mai barin-gado

Donald Trump ya bar karagar mulki ya na shekara 77, kusan daidai da shugaba Ronald Reagan.

6. Bayan shekaru 34

Shekara 34 da suka wuce, Joe Biden ya fara fitowa takarar shugaban kasa, a wancan lokaci ya rasa tikitin jam’iyyar Democrat a hannu.

Bayan nan, Biden ya zama Sanata na shekara 37, har kuma ya rike mataimakin shugaban kasa.

A yau muka ji cewa Shugaba Donald Trump ya yi afuwa ga mutane sama da 100 kafin ya bar ofis.

A cikinsu har da fitaccen mawakin nan Lil Wayne wanda aka taba kama shi da miyagun kwayoyi a cikin jirgin sama a hanyarsa ta zuwa birnin Miami.

Haka zalika Trump ya yi afuwa ga tsohon manajan yakin neman zabensa, Steve Bannon, da kuma tsohon Magajin Garin Detroit, Kwame Kilpatrick.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel