Tsohon Ministan Wasanni Ka’oje ya mutu
- Tsohon ministan wasanni na kasa Bala Bello Ka'oje ya rasu yana da shekaru 60
- An haifi tsohon ministan a ranar 20 ga watan Satumba, 1960, an binne shi a yau Talata 19 ga Janairun 2021.
- Tsohon ministan yayi karatun injiniyancin gini a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria
Bala Bawa Ka’oje tsohon Ministan Wasanni, ya mutu yana da shekaru 60.
A cikin wata sanarwa mai taken ‘Tsohon Ministan Wasanni Ka’oje ya mutu yana da shekara 60, aka binne shi a Abuja" a ranar Talata, kakakin Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, Ademola Olajire, ya ce ’yan uwa a fannin wasanni a kasar sun shiga cikin jimami da mutuwar Ka’oje.
NFF ta samu wakilcin Babban Sakatare, Dokta Mohammed Sanusi da Shugaban Kungiyoyin Membobi, Ali Abubakar Muhammed.
KU KARANTA: 2023: Manyan jiga-jigan APC sun ba Yahaya Bello da David Umahi shawarar tsayawa takaran shugaban kasa
An binne gawarsa a Abuja a ranar Talata da rana.
Sanusi ya bayyana marigayin a matsayin "ma'aikacin gwamnati mai kima da rashin girman kai wanda ya nuna matukar kwazo da sha'awar ci gaba da kuma bunkasa wasannin Najeriya."
Bala Bawa Ka’oje wanda aka haifa a Kebbi a ranar 20 ga Satumba 1960, ya sami digiri na biyu a kan Injiniyan gini daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
KU KARANTA: An yi garkuwa da wani hakimi a Adamawa
A wani labarin daban, Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Akwa Ibom, Udo Ekpenyong ya rasu. Ekpenyong ya rasu a ranar Litinin a Uyo kamar yadda wani jami'in gwamnatin jihar Akwa Ibom ya tabbatarwa da Premium Times a ranar Talata da safe.
Jami'in wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce shugaban jam'iyyar PDP din ya rasu ne sakamakon fama da yayi da cutar korona.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng