An bindige mataimakin rajistara na FUTA har lahira

An bindige mataimakin rajistara na FUTA har lahira

- Yan bindiga sun halaka Dr Amos Arijesuyo, mataimakin rajistara na FUTO

- Marigayin ya gamu da ajalinsa ne a hanyar Illesha - Akure a ranar Asabar

- Jami'ar ta FUTO ta yi Allah wadai da harin da aka kai masa tare da addu'ar Allah ya jikansa

'Yan bindiga sun kashe Amos Arijesuyo, mataimakin rajistara na Jami'ar Kimiyya ta Tarayya da ke Akura (FUTA) a Jihar Ondo, The Cable ta ruwaito.

Arijesuyo wanda shine shugaban sashin bawa dalibai shawarwari na jami'ar ya hadu da ajalinsa ne a yayin da ya ke tafiya a motarsa a hanyar Illesha-Akure a ranar Asabar.

An bindige mataimakin rajistara na FUTA har lahira
An bindige mataimakin rajistara na FUTA har lahira. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

A cikin sanarwar da jami'ar ta fitar a ranar Litinin ta bakin mataimakin sashin watsa labarai, Adegbenro Adebanjo, ta ce marigayin yana hanyar dawowa Akure ne daga Ibadan, Jihar Oyo, yan bindigan suka tare shi.

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da nadin Nuhu Fikpo a matsayin shugaban riko na NDE

"Dr Arijesuyo yana hanayarsa ta dawowa Akure ne daga Ibadan a lokacin da ya afka hannun yan bindiga da suka tare hanyar suna fashi misalin karfe 5.30 na yamma," in ji shi.

"Yan bindigan sun bude wa motarsa wuta kuma wasu harsashen sun sami Dr Arijesuyo da direbansa. Direban ya yi kokarin ya tsere sannan aka kai su asibiti.

"Sai dai Dr Arijesuyo ya rasu sakamakon raunin bindigan yayinda direbansa na cigaba da samun sauki a asibitin.

KU KARANTA: Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ya mutu kwanaki 10 bayan rasuwar matarsa

"Jami'ar ta yi Allah wadai da wannan harin da ya yi sanadin rasuwarsa. Mutuwar Dr Arijesuyo babban rashi ne ga FUTA da malamai na Nigeria da kasahen duniya."

FUTA ta yi wa iyalansa da yan uwansa ta'aziyya tare da adduar Allah ya gafarta masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel