Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 18 a jihar Kaduna

Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 18 a jihar Kaduna

- Yayinda ake farin cikin sojoji sun kawar da yan bindiga a Birnin Gwari, ana tsoron yan sanda 18 sun bace

- Kungiyar BEPU ta ce an nemi yan sandan an rasa bayan harin da aka kai musu a hanyar Funtia

Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da jami'an yan sanda 18 a Farin-Ruwa, hanyar Birnin Gwari - Funtua a jihar Kaduna, Arewa maso yammacin Najeriya.

SaharaReporters ta ruwaito cewa yan sandan na hanyarsu ta zuwa Kano daga Minna, jihar Neja ranar Juma'a lokacin da aka bude musu wuta.

Amma majiyoyi sun bayyana cewa Sojoji sun ceto kimanin yan sanda 10 a Maganda ranar Asabar.

Shugaban kungiyar cigaban Birnin Gwari (BEPU), Barista Salisu Haruna, ya tabbatar da harin a wani jawabi.

Haruna ya ce yan sandan dake Dogon Dawa sun samu labarin hakan.

KU KARANTA: Jami'an Sojoji sun ragargaji yan bindiga a garin Birnin Gwari a jihar Kaduna

Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 18 a jihar Kaduna
Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 18 a jihar Kaduna
Source: Twitter

DUBA NAN: Yan ta'addan Boko Haram sun kwace barikin Sojoji dake Marte, Sojoji sun kwato abinsu

Yace, "Kungiyar cigaban Birnin Gwari (BEPU) ta ruwaito cewa har yanzu ba'a san idan jami'an yan sanda 18 da aka kaiwa hari a hanyar Birnin-Gwari Funtuai ranar Juma'a, 15 ga watan Junairu, 2021, suke ba.

"Yan sandan 18, wadanda ke kula da hanyar Birnin Gwari Funtua, sun gamu da hari ranar Juma'a. A lokacin da ake kawo wannan rahoto, bamu san adadin wadanda abin ya shafa ba."

"Masu idanuwan shaida na tunanin wasu cikin yan sandan sun rasa rayukansa yayinda wasu sun bace cikin daji."

"Rahotannin sun tabbatar da cewa yan sanda biyu sun yi waya domin sanar da gida cewa an kai musu hari amma basu san inda suke ba."

"BEPU na kira ga gwamnati, wacce aka saurawa hakkin kula da rayukanmu da dukiyoyinmu, ta mike tsaye domin yaki da rashin tsaro har sai an samu nasara."

A wani labarin daban, rundunar Sojin Najeriya sun kashe wasu yan bindiga a harin da aka kai musu a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar.

Aruwan ya ce rundunar mayakan sama sun hallaka yan bindiga da dama kan baburansu a Saulawa, Kuduru da Farin Ruwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel