Za'a koma makarantu ranar 18 ga watan Janairu- PTF

Za'a koma makarantu ranar 18 ga watan Janairu- PTF

-Makarantu zasu koma karatu ranar 18 ga watan janairu

-Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da korona ne ya bayyana haka

-Ya fadi hakan ne a wani shiri na gidan talabijin ranar Talata

Fadar shugaban kasa a ranar Talata ta bayyana cewa za'a koma makarantu ranar 18 ga watan janairu a duk fadin Nigeria, saidai idan ma'aikar Ilimi ta saki wani abu makamancin haka, Kamar yadda The nation ta ruwaito.

Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da korona, Dr Sani Aliyu ne ya bayyana hakan a wani shirin gidan talabijin.

KU KARANTA: Abin da ya hana Shugaban kasa tsige Buratai da ragowar Hafsun Sojojin Najeriya

Za'a koma makarantu 18 ga watan Janairu- PTF
Za'a koma makarantu 18 ga watan Janairu- PTF Source: The Nation
Source: Twitter

"A kan komawa makarantu, inaso na fayyace wani a abu, abundan ministan ilimi ya ce shine zasu waiwayi abun, bai ce za'a chanza ranar komawa ba, yace zasu waiwayi yanayin ne sannan su sanar da al'umma". A cewar Aliyu.

KU KARANTA: Zulum ya sanya yara sama da 1,000 a makaranta

A wani labarin kuma, Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yada labarai, ya ce shugaban kasa bai sallami shugabannin tsaro ba ne saboda yana hango wata nagartarsu da 'yan Najeriya basu gani.

Shehu ya sanar da hakan a wani bakuncinsa da TVC ta karba kuma jaridar Vanguard ta ruwaito.

A yayin martani ga tambayar da aka yi masa a kan abinda ya hana Buhari ya sallami shugabannin tsaro duk da yadda ake ta bukatar yayi hakan, Garba ya ce:

"Saboda yana ganin abinda masu caccaka basu gani. Yana ganin abinda mutane da yawa basu gani. Ba nadi bane mai wa'adi. Babu wata doka da tace sai shugabannin tsaro an sallamesu bayan sun kwashe shekaru biyu.

"Suna aiki ne da gamsuwar shugaban kasa. A yanzu kuwa shugaban kasan ya ce zai yi gyaran. Toh ya rage gare shi ne kawai. Ina tunanin ya dace 'yan Najeriya su bada uziri."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel