Za ku iya cira kudinku kowani lokacin: FG yayinda take shirin aron kudin da mutane suka ajiye a banki

Za ku iya cira kudinku kowani lokacin: FG yayinda take shirin aron kudin da mutane suka ajiye a banki

- Gwamnatin tarayya za ta kara tura bukatan wasu sabbin kudade cikin kasafin kudin 2021

- Ana bukatan hakan ne domin sayawa yan Najeriya rigakafin cutar Korona

- Za'a samo wadannan kudade na ta hanyar rantan kudaden yan Najeriya dake ajiye a bankuna

Masu kudaden dake ajiye a banki kuma suka dade basu waiwaya ba su kwantar da hankulansu saboda gwamnatin tarayya ta ce zasu iya cire kudadensu duk lokacin da suke bukata.

Ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana hakan yayin amsa tambayoyi lokacin taron tattauna abubuwan da kasafin kudin 2021 ta kunsa jiya, Vanguard ta ruwaito.

"Za mu yi amfani da kudade da hannun jarin da ba'a waiwaya ba cikin wani asusu na musamman. Duk lokacin da banki ta tabbatar da mutum shine ainihin mai kusi, gwamnati za ta bashi," ministar ta bayyana.

KU KARANTA: Shugabannin jami'o'i sun saba da ra'ayin ASUU kan bude jami'o'i

Za ku iya cira kudinku kowani lokacin: FG yayinda take shirin aron kudin da mutane suka ajiye a banki
Za ku iya cira kudinku kowani lokacin: FG yayinda take shirin aron kudin da mutane suka ajiye a banki Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wasu matasa sun bankawa mota jibge da shanu wuta bayan da ta buge wani yaro (Hotuna)

Mun kawo muku cewa duk da rashin amincewar masu hannun jari, gwamnatin tarayya na shirin aron kudaden yan Najeriyan da ke asusun da aka dade ba'a waiwayesu ba, da kuma kudaden masu hannun jarin da aka dade ba'a bibiya ba.

Gwamnatin zata samu daman yin hakan ne bisa dokar kudin 2020 da shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu.

Karkashin sashe na 12 na dokar, an bayyana cewa za'a iya aron kudaden masu hannun jarin da ajiyan na mutanen wanda suka kai shekaru 6 ba'a waiwaya ba.

Gwamnati tace duk kudaden da ba'a bibiya ba za'a aika su wani asusun lamuni na musamman mai suna 'Unclaimed Funds Trust Fund'.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel