Yanzu-yanzu: Wasu matasa sun bankawa mota jibge da shanu wuta bayan da ta buge wani yaro (Hotuna)
- Fusatattun matasa sun kona dabbobi da ransu a jihar Oyo ranar Litinin
- Wannan mumunan abu ya faru ne bayan hadarin motan da ya auku a garin Saki
- Matasan sun aikata hakan ne don mutum daya ya mutu sakamakon hadarin
Wasu fusatattun matasa a garin Saki, jihar Oyo, sun babbaka mota dauke da dabbobi sakamakon buge wani yaro mai suna, Ayuba Raji, da motar tayi, Sahara Reporters ta ruwaito.
An tattaro cewa wannan abu ya faru ne a Challenge junction.
Wani mazaunin garin, Kazeem Adeniyi, ya bayyanawa manema labarai a Ibadan ranar Talata cewa ginin titin da akeyi a hanyar yayi sababin hadarin.
A cewarsa, motoci sun saba bin barauniyar hanya, kuma hakan na janyo hadura.
Hakazalika ya tuhumi gudun da direbobi ke yi.
KU KARANTA: Matata tana kokarin ta kashe ni dan ta mallaki dukiyata: Magidanci ga Kotu
Wani mazaunin garin, Adekunle Lawa;. wanda aka fi sani da Saki First, ya yi Alla-wadai da yan kwantiragin da aka baiwa ginin hanyar.
Ya ce rashin kammala aikin ne ke haddasa hadura a hanyar.
Yace: "Jiya, Litinin, 11 ga Junairu, 2021, misalin karfe 10 na dare, wani hadari ya auku a Challenge junction inda akayi asaran ran wani yaro, Ayuba Raji, wanda kanin wata shahrarriyar mawakiya, Monsurat Raji, ne."
"Yaron na tuka babur ne yayinda mota mai dauke da shanu ta bugeshi."
"Sai matasa suka kona motar. Sai daga baya Saki First (Lawal) ya samu tuntubar yan sanda don su dakatad da lalacin da matasan ke yi."
"Muna jajantawa iyalan mamacin; wajibi ne masu kwangila suyi wani abu kan hanyan."
KU KARANTA: Zulum ya sanya yara sama da 1,000 a makaranta
A bangare guda, hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta ce jaruman Sojojin Najeruya sun dakile yan ta'addan Boko Haram da abubuwan da suke yi a Arewa maso gabashin Najeriya.
Amma fa duk da wannan ikirari da hukumar ke yi, har yanzu yan ta'adda na kai hare-hare yankin Arewa maso gabas.
Ba da dadewa ba yan ta'addan Boko Haram suka kai hari kan manoma a Zabarmari, a jihar Borno inda suka kashe akalla manoma 40.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng