Wasu al'adu 7 masu matukar bada mamaki a Afrika

Wasu al'adu 7 masu matukar bada mamaki a Afrika

- Nahiyar Afrika tana da kabilu masu tarin yawa kuma da al'adu masu bada mamaki

- Wasu daga cikin al'adun sun samu asali ne tun kafin zuwan wayewar yankunan

- Al'adun sun hada da sharo, hawan kaho, satar matar aure, tsarkake mamaci da sauransu

Afrika tana cike da al'adu masu tarin bada mamaki amma kuma wasu daga ciki duniya bata san da su ba.

Wasu daga cikin al'adun nahiyar masu bada mamaki sun matukar dadewa domin sun zo tun kafin wayewa.

Ga wasu daga cikin ala'adun da kuma kabilun da ke yinsu.

Wasu al'adu 7 masu matukar bada mamaki a Afrika
Wasu al'adu 7 masu matukar bada mamaki a Afrika. Hoto daga Pulse.ng
Source: UGC

1. Satar matar aure - Nijar

Akwai wata kabila mai suna Wodaabe da ke kasar Nijar a yammacin Afrika. An san su da satar matan junansu. A auren farko na 'yan kabilar, ana auren zumunci ne kuma iyaye ke shirya shi tun yara suna kakana.

Amma kuma, a shagalin Gerewol na kowacce shekara, mazan kan saka kayan al'ada tare da kwalliya inda suke rawar burgewa domin satar matan wasu.

2. Tofar da yawu a matsayin gaisuwa - Kabilar Maasai

Ana samun kabilar Maasai a kasashen Kenya da Tanzani. Suna tofar wa da juna yawu a matsayin hanyar gaisuwa.

Baya da haka, idan aka haifa jinjiri, dole ne babban magidanci ya tofa masa yawu. A yadda suka yadda, hakan zai kare dan daga miyagun aljanu.

3. Tsarkake mamaci - Malawi

Yankin Chewa yana dauke da 'yan kabilar Bantu da ake samu a Malawi. A yayin bikin mutuwa, al'ada ce ta dole a wanke gawar.

Daga nan sai a dauketa a kaita wani wuri mai tsarki inda ake tsaga makogwaronta sannan a zuba ruwa a wanke. Ruwan ake amfani da shi wurin dora sanwa.

KU KARANTA: Na halaka mahaifiyata ne saboda mayya ce, Sojan da ya tsere daga wurin aiki

4. Hawan kaho a Ethiopia

A kasar Ethiopia, samari kan yi wasu gwaje-gwaje domin tabbatar da mazantakarsu. yaro ya kan cire kaya yayi tsirara inda zai kwasa da gudu ya haye kahon namijin sanuwa.

Ana kiran wannan lamarin da Hamar.

5. Gwajin yuwuwar haihuwa a Uganda

Kabilar Banyankole karamar kabila ce a Uganda. Nauyin aure ya kan rataya a kan 'yar uwar mahaifiyar amaryar.

A yayin da za a yi aure, kanwar mahaifiyar amarya za ta sadu da ango sannan kuma ta tabbatar da budurcin amaryar.

6. Shadi ko Sharo a kabilar Fulani

An san kabilar Fulani da shadi ko sharo kafin aure. A nan, angon zai sha duka daga wani babba a yankin domin samun mata da kuma mutunci.

Idan angon ya kasa jurewa, sai a fasa auren kwata-kwata.

7. Jan lebe - Ethiopia da Sudan

Kabilar Surma da ake samu a yankin kudancin Sudan da Kudu maso yamma na Ethiopia sun saba wannan dabi'ar.

Mata masu karancin shekaru suna tala lebensu ta yadda duk shekara zai kara girma.

KU KARANTA: Dalla-Dalla: Sojin saman Najeriya sun kai farmaki maboyar ISWAP, sun halaka 'yan ta'addan

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta damke wani soja mai mukamin Kofur mai suna Charles Thompson a kan zarginsa da ake da sokawa mahaifiyarsa mai suna Modupe Thompson wuka sau babu adadi har ta rasu a aranar talata, 29 ga watan Disamba.

Charles wanda ya saba dukan mahaifiyarsa a kowanne fada da ya hada su ya soka mata wuka sannan ya tsere.

Rundunar 'yan sandan ta damke shi a ranar Talata, 31 ga watan Disamba, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel