'Yan Bindiga Sun Kai Hari Plateau, an Kashe Jami'in Tsaro da Fararen Hula
- Mahara sun kai hari ƙauyen Bel da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi da misalin ƙarfe 9:00 na daren Lahadi, inda suka kashe mutane
- An bayyana sunayen mutum uku da suka mutu a harin, ciki har da Emmanuel Pam Dachung mai shekara 15
- Ƙungiyar Berom Youth Moulders Association ta yi kira ga jami'an tsaro da su gano waɗanda suka kai harin tare da hukunta su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Wasu 'yan bindiga sun kashe mazauna ƙauye uku da wani jami'in tsaro yayin wani hari da suka kai ƙauyen Bel da ke yankin Sho, a ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta Jihar Plateau.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00na daren Lahadi, 8 ga watan Nuwamban 2026 lokacin da maharan suka kutsa cikin ƙauyen tare da buɗe wa mazauna yankin wuta.

Source: Twitter
Haka kuma, wasu mutane da dama sun samu raunuka yayin harin, wanda ya ƙara tayar da hankalin jama'a kan matsalar tsaro a yankin, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Yadda maharan suka kai harin
Wani mazaunin yankin mai suna Bulus Bot, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce maharan sun shigo ƙauyen cikin dare suka fara harbin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
"'Yan bindigar sun shigo ƙauyen da misalin ƙarfe 9 na dare suka buɗe wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba wuta, inda wasu suka mutu wasu kuma suka jikkata.” In ji shi.
Bot ya bayyana harin a matsayin abin tayar da hankali, yana mai cewa mazauna ƙauyen sun tsinci kansu a cikin tashin hankali lokacin da maharan suka fara harbe-harbe.
Ya ƙara da cewa wasu mutane sun samu raunuka, lamarin da ya ƙara jefa jama'ar yankin cikin fargaba kan lafiyarsu da tsaron rayukansu.
An bayyana sunayen waɗanda suka mutu
Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar Berom Youth Moulders Association, Rwang Tengwong, shi ma ya tabbatar da kisan tare da bayyana sunayen mutum uku daga cikin waɗanda suka mutu.
Ya ce waɗanda aka kashe sun haɗa da Emmanuel Pam Dachung, mai shekara 15; Joseph Gyang, mai shekara 28; da Emmanuel Yohanna, mai shekara 32.
Tengwong ya kuma yi zargin cewa wani soja yana cikin waɗanda aka kashe a harin, wanda hakan zai kai adadin waɗanda suka mutu zuwa mutum huɗu. Sai dai ba a bayyana sunan sojan da ake zargin an kashe ba.
An buƙaci jami'an tsaro su kamo maharan
Tengwong ya yi Allah-wadai da harin, inda ya bayyana kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.
Ya buƙaci jami'an tsaro su gudanar da bincike domin gano waɗanda suka kai harin tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban shari'a.
Ya kuma jaddada cewa akwai buƙatar ɗaukar matakai masu ƙarfi domin hana sake kai hare-hare kan al'ummomin yankin.

Source: Original
An kashe mutane a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu 20 bayan kai hari al’ummar Akwando da ke Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na rana, kamar yadda shugabannin wata ƙungiyar al’umma suka bayyana.
Asali: Legit.ng


