Dalla-Dalla: Sojin saman Najeriya sun kai farmaki maboyar ISWAP, sun halaka 'yan ta'addan

Dalla-Dalla: Sojin saman Najeriya sun kai farmaki maboyar ISWAP, sun halaka 'yan ta'addan

- Rundunar Operatiob Lafiya Dole ta salwantar da rayukan wasu 'yan ta'addan ISWAP a sabon hari

- Daga jiragen yaki dakarun sojin saman Najeriya suka ragargajesu a Tumbun Gini da ke tafkin Chadi

- Sojin sun tarwatsa maboyar 'yan ta'addan, kayan aiki da kuma wasu shugabanni da mayakan ta'addanci

Rundunar sojin sama ta Operation Lafiya Dole ta halaka wasu 'yan ta'addan ISWAP a wani hari da ta kai maboyarsu da ke nisan kilomita 1 na arewacin Tumbun Gini a yankin tafkin Chadi da ke Borno.

Shugaban fannin yada labaran hukumar tsaro, John Enenche, a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an kai samamen ta jiragen yakin a ranar Laraba.

Enenche, ya ce an kai hare-haren ta sama bayan bayanan da aka samu wadanda suka nuna cewa wurin ne manyan shugabannin ISWAP da mayakansu suke haduwa domin shiryawa tare da aiwatar da hare-hare.

KU KARANTA: 2023: Afenifere ta bayyana matakin da ta dauka idan Jonathan ya fito takara

Dalla-Dalla: Sojin saman Najeriya sun kai farmaki maboyar ISWAP, sun halaka 'yan ta'addan
Dalla-Dalla: Sojin saman Najeriya sun kai farmaki maboyar ISWAP, sun halaka 'yan ta'addan. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: UGC

Ya ce wurin yana dauke da gine-gine da kayan aikin mayakan ta'addancin wanda suka boye sakamakon bishiyoyin da ke wurin.

"Harin ya tagayyara yankin inda gine-ginensu suka lalace sannan wasu mayakansu suka mutu yayin da wasu suka tsere.

"Daga bisani, sauran mayakan ta'addancin da suka tsere an sake taresu inda aka sakar musu ruwan wuta," yace.

KU KARANTA: Bidiyon mayakan ISWAP suna kashe wasu 'yan Najeriya 5 ya gigita jama'a

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, hedkwatar tsaro ta ja kunnen 'yan ta'adda, 'yan bindiga , masu garkuwa da mutane da duk wasu masu aikata laifi da ke sassan kasar nan da su tuba tare da gujewa aikata laifukan kafin dakarun sojin su far musu a 2021.

Shugaban fannin yada labarai na dakarun sojin, Manjo Janar John Enenche, a wani taron manema labarai a Abuja, ya ce a tudu, iska da ruwa duk sun fara sauya salon yakar 'yan ta'adda da masu kai musu bayanai, The Nation ta ruwaito.

Ya ce, "Mayakan ta'addancin Boko Haram, 'yan bindiga da dukkan sauran masu laifuka gara su tuba a yayin da za mu shiga 2021. Babu shakka sakon da muke da shi ga 'yan ta'adda shine, kai tsaye kun saka hannu a tikitin mutuwarku saboda aiki ne da dole mu aiwatar."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel