Na halaka mahaifiyata ne saboda mayya ce, Sojan da ya tsere daga wurin aiki

Na halaka mahaifiyata ne saboda mayya ce, Sojan da ya tsere daga wurin aiki

- Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta damke wani soja mai mukamin Kofur da laifin kisan mahaifiyarsa

- Charles Thompson ya saba dukan mahaifiyarsa a duk lokacin da fada ya hada su amma sai ya soka mata wuka a ranar

- Sojan da ya bar wurin aikinsa ba tare da sanin hukuma ba, ya ce mahaifiyarsa mayya ce shiyasa ya kasheta

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta damke wani soja mai mukamin Kofur mai suna Charles Thompson a kan zarginsa da ake da sokawa mahaifiyarsa mai suna Modupe Thompson wuka sau babu adadi har ta rasu a aranar talata, 29 ga watan Disamba.

Charles wanda ya saba dukan mahaifiyarsa a kowanne fada da ya hada su ya soka mata wuka sannan ya tsere.

Rundunar 'yan sandan ta damke shi a ranar Talata, 31 ga watan Disamba, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

A yayin zantawa da manema labarai, Charles ya tabbatar da cewa ya kashe mahaifiyarsa saboda mayya ce.

KU KARANTA: 2023: Afenifere ta bayyana matakin da ta dauka idan Jonathan ya fito takara

Na halaka mahaifiyata ne saboda mayya ce, Sojan da ya tsere daga wurin aiki
Na halaka mahaifiyata ne saboda mayya ce, Sojan da ya tsere daga wurin aiki. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

"An kama ni sakamakon laifin kisan kai da nayi. Mahaifiyata ta mutu a hannuna yayin da muke fada. Na sha ganinta tana komawa jemage da dare, lamarin da ke ci min tuwo a kwarya.

"Tana bayyana kuma ta bace. A lokacin da na shiga daki na ganta da yaro mai shekaru 10. Hakan ne yasa muka fara fadan," yace.

Charles ya yi ikirarin cewa ya dauka hutu ne saboda bashi da lafiya amma bincike ya nuna cewa barin wurin aiki yayi.

"A halin yanzu na dauka hutu ne saboda bani da lafiya. Na fadi ne yayin wani hari da aka kawo mana a Maiduguri. Ba a kore ni daga aiki ba," yace.

Thompson wanda yace mahaifinsa ya bar mahaifiyarsa tare da sauran 'yan uwansa sama da shekaru 20, ya zargi cewa mahaifiyarsa bata taba sonsa ba.

'Yan sanda sun tabbatar da cewa za su kai shi kotu bayan sun kammala bincike.

KU KARANTA: Saraki: Dalilin da yasa majalisa karkashin mulkina ta ki amincewa da wasu nade-naden Buhari

A wani labari na daban, kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta bayyana bidiyon yadda ta halaka wasu Kiristoci da ta cafke a cikin kwanakin nan a arewa maso gabas na kasar nan.

Bidiyon ya fita a ranar Talata a sa'ar da bangaren Shekau na Boko Haram suka halaka wasu mafarauta 7 a Borno sannan suka raunata wasu 19.

A bidiyon mai tsayin dakika 49, an ga 'yan ta'addan inda suka rufe fuska a tsaye dauke da bindigogi da kuma wasu mutane gurfane a gabansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: