Jami'an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutanen da aka sace a titin Kaduna-Abuja

Jami'an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutanen da aka sace a titin Kaduna-Abuja

- Titin Kaduna zuwa Abuja ta yi kaurin suna da yan fashi da masu garkuwa da mutane

- Lokuta bila adadin, an yi garkuwa da yan Najeriya da dama, ciki har da jami'an tsaro

- Hafshoshin sojin sama sun gudanar da atisayen taimakawa wajen ceto a titin

Hukumar mayakan saman Najeriya NAF ta gudanar da atisayen na musamman kan yadda ake ceto mutane a titin Kaduna zuwa Abuja.

An gudanar da atisayen ranar Asabar, 2 ga watan Junairu, 2021 domin horar da jami'an hukumar kan yaki a kasa.

An gudanar da atisayen mai take "Taimako yazo" a titin Kaduna-Abuja.

Kakakin hukumar NAF Air Vice Marshal Ibikunle Daramola, ya bayyana hakan a shafin hukumar na Tuwita.

A jawabin da yayi, babban hafsan sojin saman, Air Marshal Sadiq Abubakar, yace horar da jami'an hukumar na da muhimmanci domin samun nasara wajen yaki da ta'addanci.

Yace: "Gaba daya manufarmu shine tabbatar da cewa jami'anmu sun kware wajen artabu (da makiya)."

"Hakazalika, atisayen yau wanda aka gudanar kan yadda ake lalube da ceto mutane an yi shi domin inganta kwarewan jami'anmu wajen ceto abokan aikinsu da suka sauka daga cikin jiragensu domin wani aikin gaggawa."

Kalli hotunan atisayen:

Jami'an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutanen da aka sace a titin Kaduna-Abuja
Jami'an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutanen da aka sace a titin Kaduna-Abuja Hoto: Nigerian Air Force HQ
Source: Facebook

KU KARANTA:Jami'an yan sanda sun dakile harin yan bindiga, sun ceto wanda aka sace

Jami'an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutanen da aka sace a titin Kaduna-Abuja
Jami'an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutanen da aka sace a titin Kaduna-Abuja Hoto: Nigerian Air Force HQ
Source: Facebook

KU KARANTA: Ka samawa matasa aiki ko ayi maka juyin mulki, Father Mbaka ga Buhari

Jami'an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutanen da aka sace a titin Kaduna-Abuja
Jami'an sojin sama sun gudanar da atisayen ceton mutanen da aka sace a titin Kaduna-Abuja Hoto: Nigerian Air Force HQ
Source: Facebook

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel