Jami'an yan sanda sun dakile harin yan bindiga, sun ceto wanda aka sace
Jami'an yan sanda a jihar Zamfara sun dakile harin da yan bindiga suka kai wani gari dake wajen karamar hukumar Shinkafi ta jihar.
A cewar kakakin yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce wannan abu ya auku ne misalin karfe 4:30 na daren Asabar, ChannelTV ta ruwaito.
SP Shehu ya ce hukumar ta samu labarin cewa yan bindiga sun dira wajen Shinkafi da niyyar garkuwa da mutanen garin
Amma hadakar jami'an PMF/CTU na atisayen “Operation Puff Adder” sun far musu kuma suka kawar da su.
Hakazalika, an ceto wani matashi, Sama'ila Langa, wanda akayi garkuwa da shi a lokacin.
Tuni an mayar da shi wajen iyalansa.
KU DUBA: APC ta sanar da ranar da za a yi rajistar mambobi
KU KARANTA: Ka samawa matasa aiki ko ayi maka juyin mulki, Father Mbaka ga Buhari
A wani labarin daban, Francis Erhabor, DPO na Itam, jihar Akwa Ibom, wanda akwa ruwaito ya ki karban cin hancin N864m a cikin shekaru uku, na tunanin ajiye aikin saboda rashin adalcin da ake masa.
A ranar Asabar, an samu rahotannin cewa DSP Erhabor ya yi murabus daga aikin yan sanda saboda wasu miyagu dake hanashi cigaba a hukumar.
Rahotannin sun bayyana cewa jami'in ya ajiye aikin ne saboda yadda ake karawa sa'o'insa girma amma shi yana waje daya.
Amma daga baya an samu labarin cewa bai yi murabus ba tukun amma yana tunanin yin hakan shi yasa ya dauki hutun kwanaki uku domin yanke shawara, The Cable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng