Karin mutum 712 sun kamu da korona a ranar Kirsimeti, 4 sun mutu

Karin mutum 712 sun kamu da korona a ranar Kirsimeti, 4 sun mutu

- Hukumar NCDC ta sanar da samun karin mutum 712 da suka kamu da annobar korona

- Wadanda suka kamu sun fito ne daga jihohi 20 na kasar

- A yanzu jimlar mutane 82747 ne suka harbu da cutar a kasar, yayin da 1,246 suka mutu, an kuma sallami 70,239

Hukumar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ta bayyana cewa an samu karin mutane 712 da suka kamu da annobar korona a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba.

Hakan na kunshe ne a cikin sabbin alkaluman da hukumar ta wallafa a shafin Twitter. Ta kuma bayyana cewa karin mutane hudu sun mutu.

KU KARANTA KUMA: Daga yanzu sai sabbin ma’aurata sun nemi izini daga gwamnati kafin biki a Lagas

Karin mutum 712 sun kamu da korona a ranar Kirsimeti, 4 sun mutu
Karin mutum 712 sun kamu da korona a ranar Kirsimeti, 4 sun mutu Hoto: @NCDCgov
Source: Twitter

Sabbin mutanen da suka kamu sun fito ne daga jihohi 20 na kasar da suka hada da:

Legas: 388

Abuja: 77

Kwara: 39

Katsina: 35

Bauchi: 33

Plateau: 22

Ogun: 18

Akwa Ibom: 16

Delta: 13

Kaduna: 12

Osun: 12

Yobe: 11

Sokoto: 10

Kebbi: 8

Enugu: 6

Edo: 5

Ondo: 3

Niger: 2

Kano: 1

Oyo: 1

Gaba daya jimlar mutane 82747 ne suka harbu da cutar a Najeriya, yayin da 1,246 suka mutu sannan a yanzu an sallami mutane 70,239 bayan sun warke.

KU KARANTA KUMA: Kirsimeti: Ndume ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram suka kai kauyukan Borno da Adamawa

A wani labari, an yi ma yarima mai jiran gado na kasar saudiyya, wanda shine ministan tsaron kasar, Mohammad bin Salman, allurar cutar Korona ranar Juma'a, 25 ga watan Disamba, 2020.

Bayan da Yarima ya karbi nasa, ministan al'adan kasar, Yarima Badr Farhan, ya karbi nashi rigakafin.

Ministan lafiyan kasar, Dakta Tawfiq Al-Rabiah, ya godewa yariman bisa mulkin da ya nuna wajen samarwa al'ummar kasar rigakafin.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel