Kirsimeti: Ndume ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram suka kai kauyukan Borno da Adamawa

Kirsimeti: Ndume ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram suka kai kauyukan Borno da Adamawa

- Sanata Ali Ndume ya yi watsi da hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai jihohin Adamawa da Borno

- Yan ta'addan sun kai harin ne a daren ranar Kirsimeti

- Ndume ya kuma mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa ransu a harin

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan rundunar soji, Sanata Ali Ndume, a ranar Juma’a, ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram a kauyen Pemi da ke jihar Borno da garin Garkida da ke karamar hukumar Gumbi jihar Adamawa a daren Kirsimeti.

Garin Garkida ya kasance daya daga cikin wuraren da mishan suka fara zama a arewacin Najeriya.

Makasan sun bad da kamanni a matsayin masu aikin leburanci, a cewar wani dan shekara 24 da ya tsira daga kisan gillar.

Kirsimeti: Ndume ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram suka kai kauyukan Borno da Adamawa
Kirsimeti: Ndume ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram suka kai kauyukan Borno da Adamawa Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Ndume da yake martani a kan mummunan al’amarin, ya bukaci rundunar soji da ta zama a ankare maimakon mayar da martani bayan aikin gama ya gama.

Ya kuma mika ta’aziyya ga iyalan mamatan da shugabannin addinin da aka lalata musu cocinansu a yayin harin.

KU KARANTA KUMA: Abun mamaki: Musulmai sun je coci domin taya Kiristoci bikin Kirsimeti (hoto)

Ya bukace su da su ci gaba da addu’a don dorewar zaman lafiya a kasar.

Ndume ya ce: “Wannan abun bakin ciki ne cewa yan ta’adda sun sake kai hari a ranar Kirsimeti sannan suka kashe mutum biyar a Pemi.

“An ce an lalata cocina, asibitoci da makarantu a yayin harin.

“Ina amfani da wannan damar wajen mika jaje ga iyalan mamatan yayinda ya kamata sojoji da ke yankin su dunga kasancewa a ankare da yan ta’addan maimakon yin martani bayan aikin gama y agama.”

Rahotanni daga yankin Garkida ya nuna cewa yan ta’addan sun kai mamaya garin ne ta babban hanyar da ke sada yankin da Biu a jihar Borno.

Mutanen yankin sun bayyana cewa an tursasa jama’a tserewa daga garin zuwa tsaunuka yayinda yan ta’addan suka sace kayayyakin abinci da kona gidaje a tsaka da harbi.

A gefe guda, wasu yan ta'addan Boko Haram sun kashe mutane shida kuma sun banka wuta a cocin EYN (Ekklesiyar Yan’uwa a Nigeria) dake unguwar Pemi, karamar hukumar Chibok, a jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Kafin ka nemi auren ƙabilar Ebira: Muhimman abubuwan da ya kamata ka sani

Yan ta'addan sun kai hari ranar Alhamis - daren ranar Kirismeti yayinda al'ummar garin ke shirye-shirye biki.

An kona akalla motoci shida da gidaje biyar mallakin cocin, TheCable ta samu bayani daga wasu mazauna garin ranar Juma'a.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel