Yariman Saudiyya, MBS, ya karbi alluran rigakafin cutar Korona

Yariman Saudiyya, MBS, ya karbi alluran rigakafin cutar Korona

- Shugaba mai matsayi bayan sarki, ya karbi alluran rigakafin COVID-19

- Saudiyya ta amince a yiwa al'ummarta alluran rigakafin da kamfanin Pfizer/Biontech ta samar

- Yayinda kasashen duniya ke rabawa al'ummarsu rigakafin, babu ko guda a Najeriya

An yi ma yarima mai jiran gado na kasar saudiyya, wanda shine ministan tsaron kasar, Mohammad bin Salman, allurar cutar Korona ranar Juma'a, 25 ga watan Disamba, 2020.

Bayan da Yarima ya karbi nasa, ministan al'adan kasar, Yarima Badr Farhan, ya karbi nashi rigakafin.

Ministan lafiyan kasar, Dakta Tawfiq Al-Rabiah, ya godewa yariman bisa mulkin da ya nuna wajen samarwa al'ummar kasar rigakafin.

A ranar 17 ga Disamba, Saudiyya, ta kaddamar da baiwa al'ummar kasar rigakafin COVID-19 inda ministan lafiyan kasar, Tawfiq Al-Rabi'ah, ya fara yi.

KU KARANTA: Buhari ya aikewa Kwankwaso ta'ziyyar rasuwan mahaifinsa, Makaman KarayE

Yariman Saudiyya, MBS, ya karbi alluran rigakafin cutar Korona
Yariman Saudiyya, MBS, ya karbi alluran rigakafin cutar Korona Hoto: SPA photo
Source: UGC

KU KARANTA: Attajiri dan jihar Katsina, Dahiru Mangal, na daukan nauyin yakin neman zaben shugaban kasa a Nijar

A Najeriya, dirakta Janar na hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC), Dr. Chikwe Ihekweazu, a ranar Alhamis ya ce rigakafi ne hanya daya tilo na kawo karshen annobar Korona.

Ya yi bayanin cewa hanyoyin dakile yaduwar cutar irinsu wanke hannu, amfani da sinadarin tsaftace hannu, amfani da takunkumin rufe baki da baiwa juna tazara, kawai zasu iya rage yaduwar ne amma ba zasu iya kawo karshen annobar ba.

Ihekweazu ya kara da cewa hukumar NSCDC, kwamitin PTF da ma'aikatar lafiya zasu ilmantar da yan Najeriya kan muhimmancin rigakafi, wanda za'a samu watanni ukun farkon shekarar 2021.

A bangare guda, Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyanawa majalisar dattawa cewa gwamnatin tarayya na bukatar N400bn domin siyawa yan Najeriya rigakafin cutar Korona

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel