Daga yanzu sai sabbin ma’aurata sun nemi izini daga gwamnati kafin biki a Lagas

Daga yanzu sai sabbin ma’aurata sun nemi izini daga gwamnati kafin biki a Lagas

- A sabuwar dokar gwamnatin Lagas sai sabbin ma'aurata sun nemi izini kafin su tara jama'a a wajen biki

- Hakan na daga cikin matakan yaki da annobar korona

- Daga yanzu mutane 300 ne kadai za su halarci taron biki kuma sai sun kiyaye dokokin dakile cutar

Gwamnatin jihar Lagas ta kafa wata sabuwar doka da ya gindayawa sabbin ma’aurata neman izini daga gareta kafin kafin su tara jama’a domin yin shagalin biki.

Wannan sabon matakin yana kunshe ne a cikin wani bayani da gwamnatin ta fitar a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba mai taken “Ku zauna a gida.”

KU KARANTA KUMA: Gbajabiamila ya mika ta’aziyya ga iyalan Sheikh Lemu da na Kwankwaso

Daga yanzu sai sabbin ma’aurata sun nemi izini daga gwamnati kafin biki a Lagas
Daga yanzu sai sabbin ma’aurata sun nemi izini daga gwamnati kafin biki a Lagas Hoto: @jidesanwoolu
Source: Twitter

Wani bangare na jawabin na cewa:

“Bikin aure da kum taron jama’a kar su wace 300 bayan an samu amincewar hukumar kiyaye lafiya ta jihar Lagas.”

Shugaban hukumar kariya ta jihar Lagas, Lanre Mojola, ya bayyana cewa neman izinin kyauta ne, inda sabbin ma’auratan za su je shafin hukumar domin yin rijista.

Ya kara da cewa jami’an kiyaye lafiya za su je wuraren taron domin tabbatar da cewa an bi ka'idojin kare kai daga kamuwa da cutar korona.

KU KARANTA KUMA: Kirsimeti: Ndume ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram suka kai kauyukan Borno da Adamawa

A wani labari, Dirakta Janar na hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC), Dr. Chikwe Ihekweazu, a ranar Alhamis ya ce rigakafi ne hanya daya tilo na kawo karshen annobar Korona, The Nation ta ruwaito.

Ya yi bayanin cewa hanyoyin dakile yaduwar cutar irinsu wanke hannu, amfani da sinadarin tsaftace hannu, amfani da takunkumin rufe baki da baiwa juna tazara, kawai zasu iya rage yaduwar ne amma ba zasu iya kawo karshen annobar ba.

Ihekweazu ya kara da cewa hukumar NSCDC, kwamitin PTF da ma'aikatar lafiya zasu ilmantar da yan Najeriya kan muhimmancin rigakafi, wanda za'a samu watanni ukun farkon shekarar 2021.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel