Gbajabiamila ya mika ta’aziyya ga iyalan Sheikh Lemu da na Kwankwaso

Gbajabiamila ya mika ta’aziyya ga iyalan Sheikh Lemu da na Kwankwaso

- Femi Gbajabiamila ya yi alhinin mutuwar Sheikh Ahmed Lemu da Musa Sale Kwankwaso

- Kakakin majalisar ya yiwa mamatan samun jin kai daga Allah madaukakin sarki tare da samun Aljanna

- Gbajabiamila ya bayyana cewa ba za a taba mantawa da gudunmawar da mamatan suka bayar wajen ci gaban kasar ba

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayi Sheikh Ahmed Lemu.

Ya kuma yi ta’aziyya ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan mutuwar mahaifinsa, Alhaji Musa Sale Kwankwaso.

A wata sanarwa dauke da sa hannun mai bashi shawara na musamman a kafofin watsa labarai a ranar Juma’a, Gbajabiamila ya bayyana marigayi shehin malamin wanda yayi rayuwa mai nagarta.

Gbajabiamila ya mika ta’aziyya ga iyalan Sheikh Lemu da na Kwankwaso
Gbajabiamila ya mika ta’aziyya ga iyalan Sheikh Lemu da na Kwankwaso Hoto: @femigbaja
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Kirsimeti: Ndume ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram suka kai kauyukan Borno da Adamawa

Ya bayyana cewa Sheikh Lemu, babban alkalin jihar Neja, ya yiwa al’umma hidima, inda ya kara da cewa ya kasance mutum mai aiki don hadin kai da zaman lafiya.

Gbajabiamila ya kuma bayyana cewa za a dunga tuna marigayin saboda gudunmawarsa ga addinin Islama da fannin ilimi, ba wai a jihar Niger kadai harma ga kasar baki daya.

Kan rasuwar mahaifin Kwankwaso, kakakin majalisar ya bayyana cewa Makaman Karaye ya yi rayuwa mai cike da nasara, indaa ya kara da cewa rashinsa abune mai matukar ciwo.

Ya yi addu’an Allah ya ji kan Sheikh Lemu da Alhaji Musa Saleh Kwankwaso a Jannatul Firdaus, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Abun mamaki: Musulmai sun je coci domin taya Kiristoci bikin Kirsimeti (hoto)

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya jajantawa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa rasuwasr mahaifinsa, Alhaji Musa Saleh.

Shugaba Buhari, a sakon da ya aike ranar Juma'a yace Najeriya ta yi rashin daya daga cikin masu sarautar gargajiya dake da mutunci.

Buhari a sakon da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya saki, ya ce ba za'a iya mantawa da gudunmuwar da mahaifin Kwankwaso ya bada ba wajen hadin kan al'umma da zaman lafiya.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel