Rigakafi kadai zai kawo karshen Korona, shugaban hukumar NCDC

Rigakafi kadai zai kawo karshen Korona, shugaban hukumar NCDC

- Gwamnatin tarayya ta jaddada muhimmancin rigakafin Korona ga yan Najeriya

- Ma'aikatar lafiya ta bayyana shirinta na sayo rigakafin Korona daga kamfani Pfizer

- Yayinda kasashen duniya ke rabawa al'ummarsu rigakafin, babu ko guda a Najeriya

Dirakta Janar na hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC), Dr. Chikwe Ihekweazu, a ranar Alhamis ya ce rigakafi ne hanya daya tilo na kawo karshen annobar Korona, The Nation ta ruwaito.

Ya yi bayanin cewa hanyoyin dakile yaduwar cutar irinsu wanke hannu, amfani da sinadarin tsaftace hannu, amfani da takunkumin rufe baki da baiwa juna tazara, kawai zasu iya rage yaduwar ne amma ba zasu iya kawo karshen annobar ba.

Ihekweazu ya kara da cewa hukumar NSCDC, kwamitin PTF da ma'aikatar lafiya zasu ilmantar da yan Najeriya kan muhimmancin rigakafi, wanda za'a samu watanni ukun farkon shekarar 2021.

Yace: "Babu wani magani a tarihin likitanci, babu ko guda, da ya kare rayuka a tarihin dan Adam kamar rigakafi."

"Rigakafi kawai wasu abubuwan ban mamaki ne a fannin Likitanci. Mun kawo karshen cutar shan inna da bakon dauro gaba daya."

KU DUBA: Attajiri dan jihar Katsina, Dahiru Mangal, na daukan nauyin yakin neman zaben shugaban kasa a Nijar

Rigakafi kadai zai kawo karshen Korona, shugaban hukumar NCDC
Rigakafi kadai zai kawo karshen Korona, shugaban hukumar NCDC
Asali: Twitter

KU KARANTA: An kuma, sama da mutane 1100 sun kamu da cutar Korona ranar Laraba

A bangare guda, Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyanawa majalisar dattawa cewa gwamnatin tarayya na bukatar N400bn domin siyawa yan Najeriya rigakafin cutar Korona.

Ya bayyana haka ranar Talata, 22 ga watan Disamba, 2020 a birnin tarayya Abuja, The Nation ta ruwaito.

Ehanire ya ce gwamnatin tarayya na shirye da sayan rigakafin COVID-19 domin ceton rayuka amma ana bukatar N400 billion domin sayan rigakafin kashi 70 na al'ummar Najeriya milyan 200 akan farashin $8 ga kowani mutum.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng