Bayan kwanaki 12, gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu ya warke daga Coronavirus

Bayan kwanaki 12, gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu ya warke daga Coronavirus

- A rana guda, gwamnonin Najeriya biyu sun samu waraka daga cutar Korona

- Yayinda gwamnan Plateau ya samun waraka da safe, Sanwo-Olu na Legas ya samu da rana

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya samu waraka daga cutar COVID-19, bayan kwanaki 12 a killace.

Gwamnan ya kamu da cutar ne ranar 12 ga Disamba, 2020.

Sakataren yada labaran gwamnan, Gboyega Akosile, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita ranar Alhamis, 24 ga Disamba, 2020.

Yace: "Gwamnan Legas, Mr. @jidesanwoolu, ya warke daga COVID-19. Yanzu ya fito daga inda aka killacesa,"

KU KARANTA: A ceto min diyata kaman yadda aka ceto daliban Kankara, mahaifin Leah Sharibu

Bayan kwanaki 12, gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu ya warke daga Coronavirus
Bayan kwanaki 12, gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu ya warke daga Coronavirus
Asali: Original

A wani labarin kuwa, alkaluma akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria sun nuna cewa ko shakka babu angulu ta koma gidanta na tsamiya.

Mutane 1133 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Laraba ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 80,9222 a Najeriya.

Daga cikin sama da mutane 80,000 da suka kamu, an sallami 69,274 yayinda 1236 suka rigamu gidan gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel