Muna bukatan N400bn don siyawa yan Najeriya rigakafin Korona, Ministan Lafiya

Muna bukatan N400bn don siyawa yan Najeriya rigakafin Korona, Ministan Lafiya

- Ma'aikatar lafiya ta bayyana shirinta na sayo rigakafin Korona daga kamfani Pfizer

- Yayinda kasashen duniya ke rabawa al'ummarsu rigakafin, babu ko guda a Najeriya

Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyanawa majalisar dattawa cewa gwamnatin tarayya na bukatar N400bn domin siyawa yan Najeriya rigakafin cutar Korona.

Ya bayyana haka ranar Talata, 22 ga watan Disamba, 2020 a birnin tarayya Abuja, The Nation ta ruwaito.

Ehanire ya ce gwamnatin tarayya na shirye da sayan rigakafin COVID-19 domin ceton rayuka amma ana bukatar N400 billion domin sayan rigakafin kashi 70 na al'ummar Najeriya milyan 200 akan farashin $8 ga kowani mutum.

Ya kara da cewa za'a bukaci N156 biliyan a 2021 kuma N200 biliyan a 2022.

Ministan ya kara da cewa za'a yi ajiyar rigakafin cikin firizan ajiyan da akayi amfani da su wajen ajiye rigakafin shan inna.

KU KARANTA: Zulum ya rantsar da Farfesoshi biyu a cikin shugabannin LGAs na Borno

Muna bukatan N400bn don siyawa yan Najeriya rigakafin Korona, Ministan Lafiya
Muna bukatan N400bn don siyawa yan Najeriya rigakafin Korona, Ministan Lafiya Hoto: Pfizer
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ka fito da 'yayan cikinka su taya ka yakin neman zabe a 2023, APC ga Kwankwaso

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a bangarensa ya nuna rashin yardarsa da gwamnatin tarayya kan wannan batu musamman wajen ajiya da rabawa yan Najeriya rigakafin idan aka sayo.

Ya kara da cewa ma'aikatar ta kara kaimi wajen shirya bayanai domin gamsar da su kuma ya jaddada cewa majalisar shirye take ta taimaka da kudi wajen sayo rigakafin.

Lawan yace: "Ni fa ban gamsu da jawabin da kuka gabatar ba cewa mun shirya sayan rigakafi."

"Sai kun kara gamsar da ni cewa kun shirya."

A bangare guda, gwamnatin tarayya a ranar Talata ta yi fashin baki kan jawabin kwamitin yaki da cutar Korona na ranar Litinin cewa an sake kakaba dokar kulle na tsawon makonni biyar sakamakon dawowan cutar.

Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa babu sabon dokar kulle, kawai wasu matakai aka dauka domin hana yaduwar cutar.

Ya bayyana hakan a hirar da yayi da Radio Nigeria.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel