Korona 2.0: Babu sabuwar dokar kulle, Lai Mohammed

Korona 2.0: Babu sabuwar dokar kulle, Lai Mohammed

- Gwamnatin tarayya ta bayyana jihohi uku da suka debi kaso mafi yawa wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya

- An bada umurnin rufe makarantu har sai sabuwar shekara

- Hakazalika an bada umurnin kulle gidajen rawa, kallon kwallo, da bukukuwa

Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta yi fashin baki kan jawabin kwamitin yaki da cutar Korona na ranar Litinin cewa an sake kakaba dokar kulle na tsawon makonni biyar sakamakon dawowan cutar.

Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa babu sabon dokar kulle, kawai wasu matakai aka dauka domin hana yaduwar cutar.

Ya bayyana hakan a hirar da yayi da Radio Nigeria.

Ministan ya ce sanarwar da kwamitin yaki da Korona PTF tayi a ranar Litinin, bai hada da dokar kulle ba kamar yadda wasu gidajen jaridar suka wallafa ba.

Ya kwantar da hankulan mutanen da suka kira waya a shirin domin jin gaskiyar lamarin saboda irin illan da sabuwar dokar kulle za tayi wa tattalin arzikin kasar.

Lai Mohammed ya yi bayanin cewa abinda gwamnatin tarayya tayi shine rage yiwuwan taruwar jama'a a waje guda.

"Gwamnati bata bada umurnin sabuwar kulle ba," Lai yace.

"Abinda muka yi shine mun sake dawo da tsaffin dokoki kuma mun umurci ma'aikatan gwamnatin tarayya masu mataki na 12 zuwa kasa su kasance a gida kuma zasu samu albashinsu."

KU KARANTA: Kada ku dogara da gwamnati don samun aiki, Ministan Buhari

Korona 2.0: Babu sabuwar dokar kulle, Lai Mohammed
Korona 2.0: Babu sabuwar dokar kulle, Lai Mohammed
Asali: Instagram

KU DUBA: An yi garkuwa da dogarin Minista Pantami, ya samu kubuta

A bangare guda, gwamnatin tarayya ta bayyana Legas, Kaduna da Abuja matsayin manyan cibiyoyin kamuwa da Korona.

Boss Mustapha, Sakataren gwamnatin tarayya, ya bayyana hakan ranar Litnin, 21 ga Disamba, a Abuja yayin hira da manema labarai, ThisDay ta ruwaito.

A cewar shugaban kwamitin PTF, wadannan jihohin ne suka kwashi kashi 70% na adadin masu Korona a Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel