Ka fito da 'yayan cikinka su taya ka yakin neman zabe a 2023, APC ga Kwankwaso

Ka fito da 'yayan cikinka su taya ka yakin neman zabe a 2023, APC ga Kwankwaso

- Ana musayar kalamai tsakanin jam'iyyar PDP da APC a jihar a Kano

- Tun yanzu bangarorin biyu sun fara yiwa juna barazana kan 2023

- Yayinda PDP ke suka APC da sayar da filayen gwamnati, APC na sukar PDP da sayar da gidajen gwamnati

Jam'iyyar All Progressives Congress APC a jihar Kano ranar Talata ta mayarwa tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, martani kan jawabin da yayi kan zaben 2023.

Shugaban jam'iyyar na jihar na rikon kwarya, Abdullahi Abbas, ya yi kira ga Kwankwaso cewa ya fito da yaransa na cikinsa lokacin da zai fara yakin neman zabe a 2023.

Abbas ya bayyana hakan ne yayin rantsar da kwamitocin gudanarwa na jam'iyyar a kananan hukumomin jihar 44.

Martanin ya biyo bayan jawabin da Kwankwaso yayi cewa 2023 sai dai a mutu amma ba zasu yarda da 'inconclusive' ba.

Idan za a iya tunawa, Kwankwaso ya ce jam'iyyar PDP ba zata sake yarda a maimaita mata abinda ya faru a zaben gwamna na 2019 ba inda aka ce zaben bai kammala ba 'inconclusive' a yayin da dan takararta ke kan gaba da kuri'u 26,655.

Ba tare da bata lokaci ba Abdullahi Abbas, ya mayarwa Rabiu Musa Kwankwaso martani kan maganganun da ya yi

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya rattaba hannu a kan kasafin jihar Kano na shekarar 2021

Ka fito da 'yayan cikinka su taya ka yakin neman zabe a 2023, APC ga Kwankwaso
Ka fito da 'yayan cikinka su taya ka yakin neman zabe a 2023, APC ga Kwankwaso
Asali: UGC

KU DUBA: Gwamna Ganduje ya rattaba hannu a kan kasafin jihar Kano na shekarar 2021

Har wa yau, Mista Abbas ya kuma shaidawa 'yan jam'iyyar APC cewa kada su raga wa 'yan Kwankwasiyya ko a zahiri ko gidajen rediyo inda ya ce zaben na 2023 bai za su dauke shi da wasa ba.

"Kwankwaso ya ce zaben gwamna na 2023 zai zama 'ko a mutu, ko a yi rai'. Toh, a shirye muke. Ba ragwaye bane mu. Mun shirya wa yakin. Ba mu tsoron mutuwa.

"Ga magoya bayan mu, kada ku raga wa 'yan Kwankwasiyya, idan sun zage ku a rediyo ko a zahiri, kada ku tausaya musu."

"Bari in fada muku, zamu murde zaben 2023 kuma babu abinda zai faru. Za mu maimaita abinda muka yi a mazabar Gama idan 2023 ta zo kuma ba abinda zai faru. Wannan lokacin mu ne. Wannan gwamnatin mu ne," in ji Mista Abbas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel