Zulum ya rantsar da Farfesoshi biyu a cikin shugabannin LGAs na Borno

Zulum ya rantsar da Farfesoshi biyu a cikin shugabannin LGAs na Borno

- Gwamnan jihar Borno, Fafesa Babagana Umara Zulum, ya ratsar da sabbin shugabanninn kananan hukumomi

- Daga cikin sabbin shugabannin kanananan hukumomin da aka rantsar akwai Farfesoshi biyu da wani mai digiri da digirgir

- Kazalika, Farfesa Zulum ya bayar da umarnin sakarwa kananan hukumomin kudadensu kamar yadda doka ta bukata

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jagoranci rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin kananan hukumomin jihar su 27 ciki har da Farfesoshi guda biyu da masu digirin digirgir.

Farfesoshi biyun sun hada da: Adamu Alooma, Farfesan ilimin banki da sha'anin kuɗi kuma shugaban tsangayar nazarin kimiyya a jami'a ta Maiduguri, wanda aka rantsar a matsayin shugaban karamar hukumar Damboa.

Sai kuma Ibrahim Bukar, Farfesan ilimi shima daga jami'ar ta Maiduguri, wanda aka rantsar a matsayin shugaban karamar.hukumar Gwoza.

Bikin rantsuwar ya gudana ne a dakin taro na Multipurpose dake gidan gwamnatin jihar Borno, inda gwamnan ya tunawa mahalarta taron da cewa jihar ta share sama da shekaru goma ba tare da gudanar da zaben kananun hukumomin jihar ba sakamakon rashin tsaro.

KARANTA: Kano: APC da PDP sun fara musayar yawu a kan zaben kujerar gwmna a 2023

Zulum ya rantsar da Farfesoshi biyu a cikin shugabannin LGAs na Borno
Zulum ya rantsar da Farfesoshi biyu a cikin shugabannin LGAs na Borno
Asali: Twitter

Bikin ya samu halartar manyan shugabannin jihar; tsohon gwamna Kashim Shettima, shugaban riƙon jam'iyyar APC, Ali Bukar Dalori, sauran sun haɗa da mambobi na majalisar wakilai ta tarayya da ta jaha da sauran su.

KARANTA: Lai Mohammed: Babbar nadama ta a matsayin ministan Buhari

Gwamnan ya taya sabbin zaɓaɓɓun shugabannin tare da kansilolinsu inda ya tunatar da su nauyin dake wuyansu wanda ya zama wajibi su sauke

Legit.ng ta rawaito cewa Nasir El-Rufa'i, gwamnan Kaduna, ya sauke sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar 23 a ranar Talata

Kazalika, gwamnan ya sauke shugaban hukumar CSDA tare da maye gurbinsa da Sauda Amina-Ayotebi

Gwamnan ya ce an yi sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati a jihar Kaduna.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel