Mutumin da ya kwashe shekaru 40 a kurkuku ya samu yanci bayan wacce tayi shaida kansa a kotu tace karya tayi masa

Mutumin da ya kwashe shekaru 40 a kurkuku ya samu yanci bayan wacce tayi shaida kansa a kotu tace karya tayi masa

- Wani mutumin jihar Michigan a kasar Amurka, ya samu yanci bayan kwashe kimanin shekaru 40 a gidan yari kan laifin da bai aikata ba.

- A cewar CNN, mutumin mai suna Walter Forbes ya samu yanci ne bayan matar da tayi shaida kansa ta janye maganarta saboda karya tayi.

Walter Forbes, wanda ke da shekaru 63 yanzu, ya shiga kurkuku ne yana dalibin jami'a mai shekaru 25, bayan zarginsa da kisan Dennis Hall, a shekarar 1982, ABC ta ruwaito.

Budurwa yar shekara 19 a lokacin, Annice Kennebrew, ta bada shaidan cewa ta ga Walter Forbes da wasu mutane biyu dauke da galolin mai suna watsawa a gidan, bisa rahoton da CNN ta samu.

Cikin su ukun da akayi zargi da bankawa ginin wuta wanda yayi sanadiyar mutuwar Dennis Hall, Forbes kadai aka kama da laifi, CNN ta kara.

Bayan shekaru 30 a kurkuku, mutumin ya tuntubi kungiyar kwato hakkin wadanda aka yiwa sharri, Michigan Innocent Project, kuma aka fara binciken lamarin a 2010.

Bayan shekaru bakwai a 2017, budurwar da bada shaida kansa a kotu, Annice Kennebrew, ta amince da tattaunawa da lauyan Forbes inda ya bayyana cewa an tilasta ta yi masa shaidan karya ne.

"Sun yi barazanar kashe yarana, iyayena, 'yan uwana, da ni idan ban kai kara ofishin yan sanda kuma na bada shaida a kotu ba cewa na ga Walter da wasu mutane biyu suna banka wuta," ta fadi a wani takardar da CNN ta samu.

"Duk abubuwan da na fada, duk shaidun da na basa game da gobarar karya ne," ta kara.

"A iyakan sani na, Walter bai da hannu cikin laifin."

Yayinda aka koma kotu a watan Yuni, Kennebrew ta ce ta bada shaida kansa lokacin ne saboda lokacin karamar yarinya ce mai yara kuma tana tsoro, a cewar ABN.

An saki Walter Forbes daga gidan yari ranar 20 ga Nuwamba.

"Babu wani bakin cikin da zanyi da ita kuma na yafe mata saboda ita ma tilasta ta akayi," yace.

Mutumin da ya kwashe shekaru 40 a kurkuku ya samu yanci bayan wacce tayi shaida kansa a kotu tace karya tayi masa
Mutumin da ya kwashe shekaru 40 a kurkuku ya samu yanci bayan wacce tayi shaida kansa a kotu tace karya tayi masa
Asali: UGC

KU KARANTA: A ceto min diyata kaman yadda aka ceto daliban Kankara, mahaifin Leah Sharibu

A wani labarin kuwa, masu garkuwa da da mutane a ranar Laraba sun yi garkuwa da wani dan kasuwa a garin Minjibir, tsawon kilo mita hamsin daga birnin Kano.

Yan bindigar sun yi dirar mikiya kauyen da misalin karfe 1:00 na dare, suna harbi kan mai uwa da wabi a Masaka da ke kauyen kafin dauke wani dan kasuwa, Abdullahi Kalos.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel