Masu garkuwa sun kai hari Kano, sace dan kasuwa sun kuma kone motar 'yan sanda

Masu garkuwa sun kai hari Kano, sace dan kasuwa sun kuma kone motar 'yan sanda

- Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan kasuwa Abdullahi Kalos a karamar hukumar Minjibir tare da ƙone motar yan sanda

- Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa yan sanda sun janye sakamakon anfi su karfin makamai yayin da suke maida martani

- Ba aji ta bakin rundunar yan sandan jihar ba sakamakon rashin daga waya da kakakin rundunar Abdullahi Kiyawa bai yi ba

Masu garkuwa da da mutane a ranar Laraba sun yi garkuwa da wani dan kasuwa a garin Minjibir, tsawon kilo mita hamsin daga birnin Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Yan bindigar sun yi dirar mikiya kauyen da misalin karfe 1:00 na dare, suna harbi kan mai uwa da wabi a Masaka da ke kauyen kafin dauke wani dan kasuwa, Abdullahi Kalos.

Masu garkuwa sun kai hari Kano, sun kone motocci
Masu garkuwa sun kai hari Kano, sun kone motocci. Hoto @Vanguardngr
Asali: Twitter

Shaidu sun bayyanawa majiyar Legit.ng cewa yan bindigar sun kuma kai wa yan sanda hari tare da kona musu mota.

DUBA WANNAN: 2023: APC na Kano ta yi wa Kwankwaso martani, ta ce 'za mu murde zaben kuma ba abinda zai faru'

"Da farko naji harbi da misalin 1:30 na dare, sai harbe harben ya ci gaba. Ta tagar dakina sai na ga yan sanda suna mayar da martani," wani da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaidawa majiyar Legit.ng

"Yan bindigar sun ajiye mutanen su a kowace mahada a garin. Ina tunanin suna da makamai fiye da na yan sanda tun a karshe yan sandan sun saduda.

"Da misalin 4:20 na asuba, sun kai hari kan yan sandan da ke musu kwanton bauna kusa da makarantar firamare ta Amsharu. A cikin motar akwai DPO da kan sa da kuma ragowar jami'an sa.

"Da yan sandan suka gudu, sai yan bindigar suka cinnawa motar wuta ba tare da sun yi yunkurin binsu ba."

KU KARANTA: Zulum ya karrama bataliyar sojin da Boko Haram bata taba galaba a kanta ba (Hotuna)

Wani shaidan ya bayyanawa majiyar Legit.ng cewa yan bindigar sun zo a mota kirar Hilux, da sharon guda uku da kuma babura da dama.

"Sun baro abubuwan hawan su a gonaki, suka shigo da kafa," inji shaidan.

Mai magana da yawun yan sanda Abdullahi Kiyawa bai daga kiran waya da aka masa don jin ta bakin rundunar ba.

A wani rahoton daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce duba da girman iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, Allah ne kadai zai iya tsare iyakokin yadda ya kamata, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da ya ke jawabi yayin karbar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, wadda ke jagorancin tawagar sa ido kan zabe ta ECOWAS a Nijar, Buhari ya ce zai iya duk mai yiwuwa don kawo zaman lafiya a yankin na Sahel.

A cewar sanarwar da Femi Adesina, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan labarai, shugaban kasar ya jinjinawa takwararsa na Nijar, Shugaba Muhamadou Issoufou, "don bai yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki ba don zarcewa bayan kure wa'adinsa biyu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel